Karfin Hali: Amarya ta daba wa uwar gida wuka kar Lahira mintuna kadan da kwanciya da Mijinsu

Karfin Hali: Amarya ta daba wa uwar gida wuka kar Lahira mintuna kadan da kwanciya da Mijinsu

  • Wata Amarya ta yi ƙarfin hali ta caka wa uwar gida wuka har ta mutu saboda saɓanin kwanciyar aure da suka samu da Maigida
  • Lamarin ya faru ne a jihar Ondo, kuma matar ta ce ba ta yi nufin kashe uwar gida ba, fushi ne kan abin da mijin ya mata
  • Ta ce ta jiyo uwar gida da maigida suna zaginta yayin da suke kwanciyar aure a ɗaki, kuma mijin ya barta kwance tana jiran shi

Ondo - Rebecca Nicodemus, yar kimanin shekara 25 a duniya ta daba wa Uwar Gida wuka har lahira jim kaɗan bayan kammala kwanciyar aure da Maigidansu.

The Nation ta rahoto cewa Amarya Rebecca ta shiga matsancin kishi saboda mijinta ya taso ya barta a kan gado suna tsaka da saduwar aure domin ya koma wurin uwar gidan mai suna Precious.

Kara karanta wannan

Yadda yan Najeriya ke kuka su zubda hawaye idan suka karbi tallafin N5,000, Sadiya Farouk

Rahoto ya bayyana cewa duka matan biyu na rayuwa ne a ƙaramin gida mai ɗaki ɗaya da Falo ɗaya tare da mijin su.

Jihar Ondo
Karfin Hali: Amarya ta daba wa uwar gida wuka kar Lahira mintuna kadan da kwanciya da Mijinsu Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Takaddama ta ɓarke tsakanin matan lokacin da marigayya Precious ta fito daga ɗakin da suka yi kwanciyar aure da Maigida.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Lamarin ya faru ranar 4 ga watan Fabrairu da kusan misalin ƙarfe 5:00 na Asuba a sansanin Idogun dake kan hanyar Ode-Irele a jihar Ondo.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Tuni yan sanda suka yi ram da Amarya Rebecca kuma aka gurfanar da ita gaban Kotun Majirtire dake Akure kan tuhuma ɗaya, "Kisan kai."

A rahoton farko da yan sanda suka haɗa, Matar da ake zargin ta ce ba yi nufin ta kashe Uwar gidan ba.

Tribune Online ta rahoto A jawabinta ta ce:

"Na zo jihar Ondo ne a watan Janairu, 2022, muna rayuwa a gida ɗaya. Ina sana'ar noma kuma ina da kyakkyawar alaƙa da marigayya."

Kara karanta wannan

Rikita-Rikita: Matar aure ta kai karar mijinta Kotu saboda ya ki amince wa da auren su

"A wannan baƙar rana, ina tare da mijin mu, muna tsaka da soyewa sai ya nemi uzuri ya fita. Ina jiransa sai na ji ya koma kan abokiyar zama na suna mu'amalar aure a ɗakin kwana, na ji suna zagi na."
"Na jira suka gama ta fito, sai na tambayeta kan kalaman rashin mutuncin da ta faɗa, maimakon ta bani hakuri sai ta cacumeni da faɗa. Ni kuma na ɗauki wuka na caka mata a baya. Ban so kashe ta ba."

Mai gabatar da ƙara na hukumar yan sanda, Obadasa Ajiboye, ya shaida wa kotu cewa wacce ake kara ta caka wa marigayyi wuka a kuiɓin bayanta na hagu. hakan ya yi sanadin mutuwarta.

Wane mataki Kotu ta ɗauka?

Alkalin Kotun, Mai Shari'a, Damilola Sekoni, ya uamrci yan sanda du tsare matar kuma ya ɗage zaman zuwa 22 ga watan Fabrairu domin yanke hukunci.

A wani labarin kuma Abokanan Juna 4 sun lakaɗawa matashi duka har ya mutu kan zargin ya saci waya, Daga baya anga wayar a kujera

Kara karanta wannan

Kaduna: Kotun Shari'a Ta Tura Kishiyoyi 2 Zuwa Gidan Yari Saboda Faɗa Kan Mijinsu, Mijin Ya Ce Akwai Yiwuwar Ya Sake Su Duka

An gurfanar da wasu abokanai hudu a gaban alkalin kotun Majistire dake Yola bisa zargin azabtar da wani matashi da duka har ya mutu.

Rahoto ya nuna cewa sun halaka mutumin ne bisa zargin ya saci wayar ɗaya, amma daga baya an gano wayar ba shi ya ɗauka ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel