Matashi Ya Garzaya Masallaci Bayan Ya Lashe miliyan N38 A Caca Da Ya Buga Da N800, Bidiyon Ya Yadu

Matashi Ya Garzaya Masallaci Bayan Ya Lashe miliyan N38 A Caca Da Ya Buga Da N800, Bidiyon Ya Yadu

  • Allah ya azurta wani matashi a tashi guda bayan ga lashe zunzurutun kudi har miliyan N38 ta hanyar buga cacan N800 kacal
  • Yan taya murna sun yiwa garinsa tsinke yayin da mutane suka mamaye wajenbuga cacar don ganewa idanunsu
  • Jama'a sun kuma yiwa matashin miloniyan wanda ke cike da nutsuwa rakiya zuwa masallaci

Wani matashi ya zama miloniya a dare daya bayan ya lashe makudan kudade har naira miliyan 38 a wani gidan buga caca.

Dan Najeriyan wanda ya taki sa'a ya buga cacar na naira 800 kacal.

Matashi ya ci caca
Matashi Ya Garzaya Masallaci Bayan Ya Lashe miliyan N38 A Caca Da Ya Buga Da N800, Bidiyon Ya Yadu Hoto: @bod_republic
Asali: Twitter

A wani dan gajeгел bidiyo da @bod_republic ya wallafa a Twitter ya nuno lokacin da labarin gagarumar nasarar da yayi ya karade garin.

Ana ta ihun murna yayin da mutane da dama suka garzaya gidan cacar don ganewa idanunsu yadda abun yake.

Kara karanta wannan

Bera ya yi batan hanya a ofishin NDLEA, ya fada dakin wiwi, abin da ya yi ya ba da mamaki

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai daukar bidiyon ya nuno nasarar mutumin da N800 da ya sa na buga cacar a kwanfutar gidan cacar.

Yan mata da dama sun mato kan sabon biloniyan yayin da yake alwala don shiga masallaci. Mutanen garinsu sun bi sbi har wajen yin ibada.

Kalli bidiyon a kasa:

Masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani

@deenayaah ta ce:

"Wannan irin babban nasara, sai naji kamar na basa kariya a wannan lokacin."

@Bogzy_Baddo ya ce:

"Baba ya ci caca ya je yayi alwala. Aikin Alhamdulillah."

@stunnastunna5L ya ce:

"Idan na karbi wannan sai na fara cin tsire kamar na 3m."

@BasitOkiji ya ce:

"Ji yadda mata ke rububinsa da dadadan sunaye."

Kyakkyawar Budurwa Mai Shekaru 38 Ta Bazama Neman Miji A Intanet,Ta Fashe Da Kuka A Bidiyo

A wani labarin, wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya mai suna Princess Mimi ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta koka kan cewa har yanzu bata auru ba duk da yawan shekarunta.

Kara karanta wannan

‘Dan Takaran Jam’iyyar NNPP ya Raba Kayan Tallafin Ga Wadanda Masifa ta Auka Masu

Matashiyar mai shekaru 38 ta wallafa wani bidiyo a TikTok inda ta dungi sharban kuka a cikin wata mota yayin da take fallasa asirin zuciyarta.

Princess ta ce zata cika shekaru 39 a bana, kuma har yanzu bata yi aure ko mallakar da nata na kanta ba kuma bata da wani tsayayye da zai fito neman aurenta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel