N-Power: Gwamnatin Tarayya za ta gwangwaje matasa 300, 000 da kudin jari inji Minista

N-Power: Gwamnatin Tarayya za ta gwangwaje matasa 300, 000 da kudin jari inji Minista

  • A yanzu ana shirin yaye sahu na B na wadanda suka yi shekaru biyu su na aikin N-Power a Najeriya
  • Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin ba wasu matasan da za su gama aikin horaswa da kuma aron kudi
  • Idan matasan sun samu horo, za su yi amfani da wannan kudi da CBN za ta bada domin su kama sana’a

Abuja - Gwamnatin Najeriya ta ce ta shigo da wani tsari domin yaye dubban matasan da ba su da aikin yi, wadanda suke kammala shirin nan na N-Power.

Jaridar Premium Times ta kawo rahoto cewa gwamnati ta fito da tsari na musamman da zai taimakawa wadannan matasan da jari na fara kasuwanci.

Ministar bada agaji da tallafin gaggawa, Sadiya Umar Farouq ta bada wannan albishir a ranar Alhamis, 17 ga watan Fubrairu 2022 ga wadannan matasan.

Kara karanta wannan

Yadda manya suka yi kokarin wanke Abba Kyari daga badakaloli amma abin ya faskara

A cewar Ministar, tsarin da aka zo da shi ga masu shirin barin aikin N-Power zai kunshi horaswa na musamman a bangarori dabam-dabam na samun kudi.

Bayan nan, gwamnati za ta raba masu kudi domin su kama wata sana’a da za ta rike su nan gaba.

N-Power
Sadiya Umar Farouq Hoto: www.npowerdg.com
Asali: UGC

An zakulo 300, 000

Wannan tsari zai shafi wadanda suka kammala shekaru biyu su na aikin na N-Power. Daga cikin mutane 500, 000 da aka dauka aikin, 300, 000 ne za su amfana.

Wadannan mutane ne suka nuna sha’awar su na bukatar wannan shiri na gaban goshi da aka kawo. Ma’aikatar za ta hada-kai da CBN ne wajen dabbaka tsarin.

Babban bankin CBN zai bada aron kudin ne domin ma’aikatar tarayya ba ta bada bashi. A karshe ana sa ran cewa wadanda ba su da abin yi, za su iya rike kansu.

Kara karanta wannan

Kisan Hausawa dillalan shanu a Kudu: Kungiyoyin Arewa sun fusata, sun tura gargadi ga gwamnatin Abia

Farouk ta yi wannan jawabin ne kamar yadda ta saba zantawa da manema labarai lokaci bayan lokaci.

“A game da wannan, mun yi nisa, har ana horas da wadanda suka nuna sha’awa, kuma na tabbata zuwa karshen rubu’in shekarar nan, CBN za ta fara ba su bashi.”

- Sadiya Umar Farouq

Binciken Obasanjo

A makon nan ne aka ji ‘Yan Majalisar dattawan kasar nan za su binciken kwangilolin N400bn da aka bada a gwamnatin Olusegun Obasanjo wanda ya bar mulki a 2007.

An fitar da makudan kudin ne domin a gina dakunan shan magani a kananan hukumomi 774. Shekaru 16 kenan, babu labarin inda kudin suka shiga, kuma babu aikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel