Yadda manya suka yi kokarin wanke Abba Kyari daga badakaloli amma abin ya faskara

Yadda manya suka yi kokarin wanke Abba Kyari daga badakaloli amma abin ya faskara

  • Ana zargin akwai wadanda suka nemi su wanke DCP Abba Kyari daga zarge-zargen da ake yi masa
  • Alal-akalla wasu sun yi ta kokari wajen nemawa jami’in tsaron sauki idan an tashi hukunta shi
  • Wannan son-kai da wasu suka kawo akasin a bi doka ya kawo rabuwar kai tsakanin PSC da NPF

Abuja - Wani rahoto na musamman da Daily Trust ta fitar a ranar 17 ga watan Fubrairu 2022, ya ce an yi kokarin ba Abba Kyari kariya daga zargin da suke kansa.

Wasu manya sun nemi su sa baki a binciken da ake yi wa DCP Abba Kyari na alaka da ‘yan damfara da ma zargin NDLEA na hannunsa wajen harkar kwayoyi.

Akwai wasu manyan jami’an tsaro da tsofaffin jami’an da suka yi ritaya da suka nemi a wanke Kyari ko kuma a nema masa sauki a binciken da ake ta yi a kansa.

Kara karanta wannan

Harkar kwaya: Abba Kyari zai iya karasa rayuwarsa ta Duniya a kurkuku a dokar NDLEA

Majiyar ta bayyana cewa wannan yunkuri ne ya jawo aka samu sabani tsakanin shugabannin hukumar PSC na kasa da jagororin rundunar ‘yan sanda na kasa.

Ran Buhari ya baci

Wannan lamari har sai da ya jawo ran Mai girma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya baci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abba Kyari
Abba Kyari a bakin aiki Hoto: DCP Abba Kyari fans
Asali: Facebook

Baya ga shugaban kasa, sauran kasashen da Najeriya ta ke hulda da su sun yi takaicin abin da ke faruwa. Duniya ta sa idanu, ta na sauraron a hukunta masu laifi.

Masu kokarin ba Kyari kariya sun yi ta jan lokaci a binciken da ake yi. Sun yi hakan ne da nufin fito da sababbin bayanai da za su zama hujjojin da za su iya kare shi.

Akwai kura-kurai a binciken - PSC

A wani rahoton da jaridar ta fitar dazu, an ji hukumar PSC ta fito tana cewa akwai matsaloli da-dama tattare da rahoton binciken da jami’an ‘yan sanda suka gudanar.

Kara karanta wannan

Ana ta bincike: Hukumar 'yan sanda ta dakatar da 2 daga cikin abokan harkallar Abba Kyari

Mai magana da yawun PSC, Ikechukwu Ani ya shaidawa 'yan jarida cewa binciken da Joseph Egbunike ya jagoranta a kan DCP Kyari dankare yake da kura-kurai.

Lamarin ya sake zani bayan da hukumar NDLEA ta fito gaban Duniya a farkon makon nan ta bayyana cewa ta na neman Kyari ya amsa tambayoyi kan harkar kwaya.

Wasu daga cikin shugabannin hukumar PSC mai kula da aikin ‘yan sandan sun ji dadin bankado wannan badakala, a gefe guda wasu manyan kasar ba su ji dadi ba.

Lamar 'Danuwan Abba Kyari ta fito

Kun ji cewa binciken ‘yan sandan ya bankado yadda Ramon Abass watau Hushpuppi da mutanensa suka rika aikawa kanin Abba Kyari kudi ta asusun banki.

Sannan binciken da aka yi ya kuma nuna DCP Abba Kyari wanda aka dakatar daga aiki ya tura N44m zuwa ga asusun wannan kanin na sa a lokuta dabam-dabam.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: NDLEA Ta Fara Yi Wa Abba Kyari Zafafan Tambayoyi a Ofishinta

Asali: Legit.ng

Online view pixel