Sadu da matashiyar da ta rubuta Al-Qur’ani mai girma cikin watanni uku

Sadu da matashiyar da ta rubuta Al-Qur’ani mai girma cikin watanni uku

  • Matashiya mai shekaru 18, Sumayyah Shuaibu Salisu ta rubuta Al-Qur'ani mai girma cikin watanni uku
  • Sumayyah wacce ta kasance diya ga Shehin Malami, Shuaibu Salisu Zaria, ta ce ta rubuta littafin mai tsarki da hannunta ba tare da taimakon wani ba
  • Matashiyar dai ita ce ta yi ta daya a gasar Al-Qur'ani hizfi 60 da tafsir na kasa da aka yi a 2021

Sumayyah Shuaibu Salisu ta kasance matashiya yar shekara 18 wacce ta haddace da kuma iya rubuta Al-Qur’ani mai girma da ka a Zaria.

Sumayya wacce aka haifa a garin Jega da ke jihar Kebbi, ta kasance diya ta uku a wajen Shehin malamin nan na Najeriya kuma mazaunin kasar Saudiyya, Shuaibu Salisu Zaria, wanda ya dawo kasar bayan kammala digirinsa na biyu a jami’ar Madina da ke Saudiya.

Kara karanta wannan

Kamar a jahiliyya: Uba ya kashe 'ya'yansa tagwaye, za a rataye shi har sai ya mutu

Sadu da Sumayyah matashiyar da ta rubuta Al-Qur’ani mai girma cikin watanni uku
Sadu da Sumayyah matashiyar da ta rubuta Al-Qur’ani mai girma cikin watanni uku Hoto: BBC/ ahmadiyya-islam.org
Asali: UGC

A wata hira da tayi da jaridar Daily Trust, Sumayyah ta ce:

“Zuwa yanzu, na rubuta cikakken Al-Qur’ani mai tsarki da hannuna ba tare da wani ya nuna mun ko na kwafa daga wani littafi ba cikin watanni uku; kuma a yanzu ina rubuta na biyu. Idan Allah ya yarda, zan kammala shi shima cikin wata daya ko fiye da haka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Rubuta Al-Qur’ani mai girma ya kasance mafarkina a kodayaushe, kuma nagode ma Allah madaukakin sarki da ya cika mun dogon burina. Ya dauke ni tsawon watanni uku kafin na rubuta cikakken Al-Qur’ani, duk da gwagwarmayar karatuna. Ka san har yanzu ina aji biyu na babban sakandare (SS2) kuma ina koyarwa a makarantar gidauniyar Al-Mu’assasa Islah a Anguwar Dan Dutse, Tudun Wada, Zaria, wacce take mallakin mahaifina.
“Na haddace Al-Qur’ani gaba dayanta tun ina yar karama, kuma a 2021 na shiga gasar Al-Qur’ani ta kasa sannan na zo ta daya a hizfi 60 da tafsiri. Na kuma shiga irin gasar a 2022 inda na zo ta uku.”

Kara karanta wannan

Kotu ta sa a yi wa matashin ɗan kasuwa Bulala Bakwai a jihar Kaduna

Daily Trust ta rahoto cewa an haifi Sumayyah, wacce ta kware a harshen Larabci a Najeriya amma ta fara karatunta na Islamiyya a Madina kafin ta dawo kasar a 2018.

Ta kuma kasance mai jawa mahaifinta baki a yayin tafsir musamman a lokacin kullen korona.

Ta kara da cewa:

“Burina na gaba shine na zama masaniyar kimiyyar kwamfuta kuma babbar malamar addinin musulunci.”

Bidiyo da hotunan gasar karatun Al-Kur'ani da rundunar 'yan sanda ta shirya a Kano a tsakanin jami'ai

A gefe guda, rundunar 'yan sandan jihar Kano ta shirya gudanar da gasar karatun Al'Kur'ani tsakanin jami'an 'yan sandan da ke aiki a jihar Kano.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a cikin wani bidiyo da ya yada a shafinsa na Facebook a ranar Laraba 17 ga watan Nuwamba, 2021.

A cewar Kiyawa, ana gudanar da gasar karatun ne a hedkwatar 'yan sanda da ke Bompai a jihar Kano, a karkashin jagorancin kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Sama'ila Shu'aibu Dikko.

Kara karanta wannan

Farfesancin Dakta Pantami: Jami'ar FUTO ta fusata, ta ce ta maka ASUU a kotu

Asali: Legit.ng

Online view pixel