Matashi a Kano,Tijjani, ya sha fiya-fiya bayan samun labarin budurwarsa zata auri maikudi

Matashi a Kano,Tijjani, ya sha fiya-fiya bayan samun labarin budurwarsa zata auri maikudi

  • Bayan samun labarin wani ya yi masa kafa a wuya, wani matashi a Kano ya nemi halaka kansa
  • Tijjani ya tsallake rijiya da baya lokacin da wasu suka kwace kwalbar daga hannunsa
  • Bayan da ya farfado, matashin ya bayyana cewa dalilin da yayi hakan shine ba zai iya rayuwa bata ba

Kano - Wani matashi a jihar Kano masi suna Tijjani Abubakar ya yi yunkurin hallaka kansa ta hanyar shan ruwan fiya-fiya ranar Talata, 15 ga watan Febrairu, 2022.

Tijjani, dan unguwar Gama a karamar hukumar Nasarawa ta jihar ya tsallake rijiya da baya.

City & Crime ta ruwaito cewa Tijjani ya yi kokarin hallaka kansa ne bayan budurwsa ta jizgashi don auren wani mutumi, wanda yafi kudi da iya soyayya.

DailyTrust ta ce wani mai idon shaida yace Abubakar mai sana'ar sayar da waya ne a Farm Center, ya sha da kyar bayan dan'uwansa ya gansa yana shan fiya-fiyan.

Yace:

"Yana ganinsa ya ruga da gudu, kuma tare da mutane suka samu damar kwace kwalbar fiya-fiyan dake hannunsa."

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tijjani
Matashi a Kano,Tijjani, ya sha fiya-fiya bayan samun labarin budurwarsa zata auri maikudi Hoto: City&Crime
Asali: UGC

Dalilin da yasa nayi niyyar halaka kaina

Kalamansa na farko bayan farfadowa, Tijjani Abubuakar ya bayyana cewa ya yanke shawarar haka ne saboda ba zai iya rayuwa ba tare da ita ba.

Yace:

"An bani labarin tana shirin auren wani, kuma har ya tura magabatansa don ganawa da iyayenta. Shi yasa na yanke shawarar yin haka."

Matashi mai shekaru 19 ya dirka wa malamar shi mai shekaru 28 ciki

Richard Nana Sam, dan kasar Ghana ne wanda ransa yayi matukar baci, sanadiyyar wani lamari dake wakana a gidan shi, wanda ya yanke shawarar fallasa wa a kafafan sada zumuntar zamani, da sa ran samun mafita.

Yayin bada labarin kalubalen da yake fuskanta a wata sananniyar kungiyar 'yan Ghana dake da shafi a Facebook, ya kwashe labarin tun daga farko har karshe.

Richard ya bayyana yadda yayi wa yaran shi tagwaye (namiji da mace) masu shekaru 19 hayar malamar da za ta dunga koya musu karatu a gida.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel