El-Rufai ya cika shekaru 62 a duniya, gwamnonin APC sun aike masa da sako

El-Rufai ya cika shekaru 62 a duniya, gwamnonin APC sun aike masa da sako

  • Gwamanan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai ya cika shekaru 62 a duniya, ya samu yabon gwamnonin APC
  • Wannan na zuwa ne yayin da gwamnonin suka aike da sakon taya shi murna da kuma yaba irin ayyukansa
  • Sun bayyana cewa, sun gamsu da yadda gwamnan ke fafutukar kawo ci gaba a jiharsa da ma kasa baki daya

Jihar Kaduna - Gwamnonin jam’iyyar APC a karkashin kungiyar Progressive Governors Forum (PGF) sun bi sahun gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, domin murnar cikarsa shekaru 62 a duniya.

Gwamnonin sun bayyana murnarsu ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar kuma gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, ya fitar a ranar Laraba a Abuja, Leadership ta ruwaito.

Gwamnan Kaduna ya cika shekaru 62 a duniya
El-Rufai ya cika shekaru 62 a duniya, gwamnonin APC sun aike masa da sako | Hoto: leadership.ng
Asali: Facebook

Sanarwar ta amince tare da yabawa jagoranci, hangen nesa da kuma jajircewar Gwamna El-Rufai na samar da dunkulalliyar Najeriya mai albarka, karkashin jagorancin jam’iyyar APC.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun bayyana dalilin kai Gwamnatin Buhari kotu, har suka yi nasara a kan ta

Muna goyon bayan ayyukan El-Rufai, gwamnonin APC

Gwamnonin jam’iyyar APC, sun jaddada aniyarsu ta hadin gwiwa wajen aiwatar da shirye-shiryen da za su karfafa karfin jihohinsu na ci gaba wajen samar da ayyukan yi, da rage rashin daidaito da kuma rage radadin talauci a Najeriya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Daily Trust ta tattaro wani yankin sanarwar da ke bayyana yabo ga gwamnan na cewa:

“Musamman muna so mu yabawa jagoranci, hangen nesa da kuma himmarka wajen ganin an samu dunkulalliyar Najeriya, a karkashin jagorancin jam’iyyar mu ta APC.
“Mun yaba da gudunmawar da kake baiwa tawagar Gwamnonin APC ta hanyar ba da haske da kuma jajircewa da ka bayar wajen tafiyar da harkokin mulki a jihar Kaduna da ma a matakin kasa baki daya."

Matar Bashir El-Rufai, Dan gwamnan Kaduna, ta haifa tagwaye maza

Kara karanta wannan

Emefiele 2023: Kusoshin APC sun dage, su na so Gwamnan CBN ya nemi Shugaban kasa

A wani labarin, Bashir El-Rufai, dan gwamnan jihar Kaduna tare da matar sa Halima Nwakego, sun samu karuwar yara maza biyu tagwaye.

Bashir ya na daya daga cikin 'ya'ya mazan gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai.

Ya wallafa labarin mai dadi a shafin sa na Twitter.

Kamar yadda wallafar ta ce:

"Godiya ta tabbata ga Allah. Matata ta haifa kyawawan tagwaye maza biyu masu kama daya. Mahaifiyar ta na cikin koshin lafiya, mahaifin ya na cike da farin ciki. Na gode wa Allah. Dukkan ikon na ka ne," ya rubuta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel