Gwamnoni sun bayyana dalilin kai Gwamnatin Buhari kotu, har suka yi nasara a kan ta

Gwamnoni sun bayyana dalilin kai Gwamnatin Buhari kotu, har suka yi nasara a kan ta

  • Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya yi karin haske a kan shari’arsu da gwamnatin tarayya
  • Shugaban NGF ya ce gwamnoni su na goyon bayan bangaren shari’a da majalisa su ci gashin kansu
  • A cewar Dr. Kayode Fayemi, sun garzaya kotu ne kurum saboda a haramta taba asusun Gwamnoni

Abuja - Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce kungiyar gwamnonin Najeriya watau NGF ta kai gwamnatin tarayya kotu ne saboda tsare dukiyoyinsu.

The Cable ta rahoto Dr. Kayode Fayemi ya na cewa gwamnoni sun kalubalanci doka mai cikakken ikon a 10 da aka kawo ne domin hana a taba masu asusunsu.

Dokar da shugaba Muhammadu Buhari ya kawo tayi nufin karfafa bangaren shari’a da ‘yan majalisa. Amma gwamnoni suka kalubalanci dokar a kotun koli.

Da yake magana a gidan talabijin na Channels a ranar Litinin, 14 ga watan Fubrairu 2022, gwamnan na Ekiti ya bayyana matsayar gwamnonin Jihohi.

Kara karanta wannan

Emefiele 2023: Kusoshin APC sun dage, su na so Gwamnan CBN ya nemi Shugaban kasa

Duk da shari’ar da suka yi da gwamnatin Muhammadu Buhari, Kayode Fayemi ya ce gwamnoni na goyon bayan a ba kowane bangare cikakken iko da kudinsa.

Gwamnan na Ekiti wanda shi ne shugaban kungiyar NGF ya ce abokan aikinsa su na kan yarjejeniyar da suka cin ma da ‘yan majalisa da bangaren shari’a.

Gwamnan Gwamnoni
Gwamna Fayemi tare da Shugaba Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Maganar Kayode Fayemi

“Bari in fada maku cewa gwamnoni su na kan yarjejeniyar da aka cin ma da wakilan bangaren shari’a da na majalisa a gaban Ministan kwadago.”
“Ba za a taba wani abu a cikin yarjejeniyar MoU da aka cin ma a wajen wannan taron ba.”
“Ba mu canza matsayarmu a kan wannan ba. Kusan kowace gwamnatin jiha a Najeriya, ta cusa wannan a kasafin kudinta na shekarar 2022.”
“Za a ba su cin gashin kansu. Ba za mu tserewa wannan matsaya da kungiyar NGF da sauran gwamnoni da ke sauran jihohi suka dauka ba.”

Kara karanta wannan

Gwamnoni da Majalisar Tarayya na neman taba karin albashin da aka yi ta bayan-fage

Dokar ta sabawa tsarin mulki

Sai dai Fayemi ya ce a tsarin damukaradiyya, ana bin doka da tsarin mulki. Shiyasa suke ganin wasu sun ba shugaban kasa gurguwar shawara a kan E.O 10.

Bayan an jawo hankalinsa, Dr. Fayemi ya ce shugaban kasa ya ba shugabannin NGF dama su zauna da Ibrahim Gambari da AGF domin a samu maslaha.

A zaman da aka yi, gwamnonin sun bayyana cewa za su je kotu ne kurum saboda gudun Buhari ya kafa tarihi, nan gaba wani gwamnati ta taba asusun jihohi.

2023 sai Emefiele

Ku na da labari cewa duk da babu ruwansa da siyasa, wasu masu rike da madafan iko sun hurowa Godwin Emefiele wuta ya fito takarar shugaban kasa a 2023.

Kira-kiraye ga Gwamnan CBN ya fito takarar shugaban kasa ya fara karfi, saboda ana kyautata zaton ya samu fada a wajen shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Kara karanta wannan

Zulum ya gina gidaje 803 a Malari ya gwangwaje wadanda suka koma da N58.5m da kayan abinci

Asali: Legit.ng

Online view pixel