Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa babban limami a Kudancin Kaduna rasuwa yana da shekaru 130

Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa babban limami a Kudancin Kaduna rasuwa yana da shekaru 130

  • Alhaji Sheikh Adam Tahir, babban limamin masarautar Jema'a a Jihar Kaduna ya riga mu gidan gaskiya
  • Sheikh Tahir ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya a Kaduna yana da shekaru 130 a duniya kamar yadda Alhaji Yakubu Isa, Dokajen Jama'a, ya tabbatar
  • Ibrahim Adam Tahir, daya daga cikin yayan marigayin limamin ya ce mahaifinsu ya haifi yara 50, amma yanzu 26 ke raye, sai jikoki 290 da tattaba kuni fiye da 2000

Jihar Kaduna - Babban Limamin Masarautar Jema'a da ke Jihar Kaduna, Alhaji Sheikh Adam Tahir ya rasu yana da shekaru 130 a duniya, Daily Trust ta rahoto.

Marigayin ya rasu ne a Kaduna a ranar Laraba bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa babban limami a Kudancin Kaduna rasuwa yana da shekaru 130
Allah ya yi wa babban limami a Kudancin Kaduna rasuwa yana da shekaru 130. Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Mataimakin Limamin Jema'a, Alhaji Muhammad Kabir D. Kassim, ya tabbatarwa wakilin Daily Trust rasuwar limamin da ya shafe shekaru yana jan sallah a babban masallacin Jema'a kuma mutumin kirki ne abin koyi.

Kara karanta wannan

Kotu ta sa a yi wa matashin ɗan kasuwa Bulala Bakwai a jihar Kaduna

A sakonsa na ta'aziyya, Mai martaba Sarkin Jama'a, Alhaji Muhammad Isa Muhammad II ya bayyana rashin limamin a matsayin babban rashi ga Masarautar Jema'a da mutanen Kudancin Kaduna.

Takardar ta'aziyyar mai dauke da sa hannun Sakataren Masarautar, Alhaji Yakubu Isa (Dokajen Jama'a) ya nuna dimauta bisa rasuwar babban limamin kuma daya daga cikin masu nada sarki.

Ya yi addu'ar Allah ya jikansa da rahama.

Marigayin ya bar yaya da jikoki da tattaba kunne

Ibrahim Adam Tahir, daya daga cikin yayan marigayin limamin ya shaida wa majiyar Legit.ng cewa mahaifinsu ya haifi yara 50, amma yanzu 26 ke raye, sai jikoki 290 da tattba kuni fiye da 2000.

Ya kara da cewa za a yi jana'izarsa a safiyar ranar Alhamis.

Matar Shahararren Tsohon Gwamnan Najeriya Ta Rasu a Asibiti a Amurka

Kara karanta wannan

Yar’adua: Mahaifyar Ɗan Takarar Gwamna a Katsina Ta Riga Mu Gidan Gaskiya

A wani labarin, Njideka Ezeife, matar tsohon gwamnan jihar Anambra wanda kuma dattijo ne a kasa, Chief Chukwuemeka Ezeife ta riga mu gidan gaskiya.

Njieka ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti da ke Amurka kamar yadda kungiyar dattawan Igbo ta sanar ta bakin sakatarenta Farfasa Charles Nwekeaku, The Sun ta ruwaito.

Nwekeaku ya ce ana sa ran tsohuwar matar gwamnan za ta dawo Najeriya ne a ranar Litinin, 13 ga watan Disamban 2021 amma kwatsam ta fara rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel