Gurbattacen Fetur: Ba mu san haka zai faru ba, a yi mana afuwa, Shugaban NNPC ya bada hakuri

Gurbattacen Fetur: Ba mu san haka zai faru ba, a yi mana afuwa, Shugaban NNPC ya bada hakuri

  • Shugaban Kamfanin tace man fetur ta Najeriya, Mele Kyari ya nemi afuwar 'yan Najeriya bisa gurbattacen man fetur da aka shigo da shi kasar
  • Kyari ya bada hakurin ne yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai na tarayya domin yin bayani game da lamarin
  • Ya ce wasu dillalan man fetur ne suka shigo da gurbattacen man, kuma hukumomin da ya dace su tantance ingancin man ba su duba ba amma hakan ba zai sake faruwa ba

FCT, Abuja - Mele Kyari, babban manajan kamfanin tace man fetur na Najeriya, NNPC, ya nemi afuwar 'yan Najeriya bisa shigo da gurbattacen man fetur, PMS, zuwa kasar.

Kyari ya bada hakurin ne a ranar Laraba yayin da ya bayyana a gaban kwamitin majalisar wakilai na tarayya kan man fetur, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Man Fetur Zai Wadata Zuwa Karshen Wata, Za Mu Raba Lita Biliyan 2, Shugaban NNPC

Gurbattacen Fetur: Ba mu san haka zai faru ba, a yi mana afuwa, Shugaban NNPC ya bada hakuri
Gurbattacen Fetur: Ba mu san haka zai faru ba, a yi mana afuwa, Shugaban NNPC ya bada hakuri
Asali: Original

Ya ce:

"Mun yi nadamar afkuwar wannan abin. Ba bu yadda muka iya, ba mu yi zaton hakan zai faru ba. Muna bawa 'yan Najeriya hakuri. Ba mu yi zaton hakan zai faru ba."

Kyari ya shaida wa yan majalisar cewa Najeriya bata gwada fetur din ba a a tashan jirgin ruwa kuma ba a gwada ba a NNPC.

Ya kara da cewa dillalan man fetur din sun musanta zargin da ake musu ne saboda gudun biyan tara.

Daga karshe ya ce NNPC ta dauki matakan ganin cewa hakan ba zai sake faruwa ba.

Dillalan man fetur ne suka shigo da mai gurbattacce, NNPC

A makon da ta gabata, hukumar kula da ingancin man fetur a Najeriya, NMDPRA, ya tabbatar da cewa an samu sinadarin methanol fiye da ka'idar da Najeriya ta tanada kuma an sake fetur din a gari.

Kara karanta wannan

Wahalar man fetur: N600 ake sayar da litan mai yanzu a Abuja

Hakan ya janyo dogayen layi a gidajen man fetur saboda da dama sun rufe gidajen man.

NNPC ta yi ikirarin dilallan man fetur masu zaman kansu hudu ne suka shigo da gurbattacen man da suka hada da MRS, Oando, Emadeb Consortium da Duke Oil, wani sashi na NNPC.

MRS, Oando da Emadeb Consortium sun musanta zargin.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel