Ku maida hankali kan Kwarewa fiye da samun takardar Satifiket, Pantami ya shawarci Matasa

Ku maida hankali kan Kwarewa fiye da samun takardar Satifiket, Pantami ya shawarci Matasa

  • Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Pantami, ya shawarci matasa sun bai wa samun kwarewa fifiko
  • Pantami yace idan matasa suka samu horo kuma suka zama gwanaye, duk wasu kalubalen kasar nan za su zama tarihi
  • Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina, ya ce an shirya wannan gasa ne domin zakulo gwanayen matasa a ƙasa

Katsina - Ministan harkokin sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Pantami, ya jaddada bukatar gwamnati a kowane mataki da makarantu su fi maida hankali kan kwarewa fiye da samun takardar shaida (Certificate).

Pantami yace hakan ba wai zai samar da ayyukan yi bane kaɗai, zai shawo kan matsalolin zaman kashe wando da kuma magance ƙalubalen da ƙasar nan ke fama da su.

Channels tv tace Ministan ya faɗi haka ne a wurin taron miƙa kyauta ga waɗan da suka samu nasara a gasar National Talent Hunt Challenge a jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari ya soke taronsa da gwamnonin APC bayan sun hallara, zai shilla turai

Isa Pantami
Ku maida hankali kan Kwarewa fiye da samun takaradar Satifiket, Pantami ya shawarci Matasa Hoto: Isa Pantami FB fage
Asali: Facebook

Bayan haka, Farfesa Pantami ya roki waɗan da suka shirya gasa su ɗauki bayanan mutanen da suka fafata domin samun saukin nemo su nan gaba.

Meyasa aka shirya gasar?

A nasa ɓangaren, Gwamna Aminu Bello Masari, ya yi bayani kan musabbabin shirya gasar da ya haɗa da ƙarin kwarin guiwa da gina kwarewar matasa a jihar da ƙasa baki ɗaya.

Masari ya ce:

"Wannan gasar zata kara ɗaga izzar jihar Katsina da kuma sanya jihar ta fita tsara daga cikin takwarorinta a ƙasar nan da ma duniya baki ɗaya."

An shirya gasar ne domin ɗaukar matakan da zasu zaƙulo yan takara masu kwarewa ba wai a jihar Katsina kaɗai ba, a ƙasa baki ɗaya.

A wani labarin na daban kuma An shiga tashin hankali yayin da tsohon Sarki Sanusi II ya shirya kai ziyara jihar Kano

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Ma'aikacin FG ya tsare matarsa da bindiga, ya nemi ta biya shi kuɗin da ya kashe a kanta

Manyan masu ruwa da tsaki da masanan tsaro sun bayyana damuwarsu game da jita-jitar tsohon Sarki zai kai ziyara jihar Kano.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa a halin yanzun ba ta da masaniya kan lamarin, idan ma dagaske ne ta na maraba da zuwansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel