Da dumi: Bidiyon lokacin da Abba Kyari ke bada cin hancin daloli don shigo da hodar Iblis ya bayyana

Da dumi: Bidiyon lokacin da Abba Kyari ke bada cin hancin daloli don shigo da hodar Iblis ya bayyana

Bidiyon hukumar NDLEA dake nuna lokacin da Abba Kyari ke kokarin baiwa jami'an hana fasa kwabrin kwayoyi kudin cin hanci ya bayyana a kafafen yada labarai.

AriseTV ta wallafa bidiyon a shafinta na Tuwita wanda ke nuna Abba Kyari da wani mutumi cikin mota suna tattaunawa da mike-miken daloli.

Rahoton yace yana kokarin bada cin hancin $61,500 daga cikin kudin da aka samu na sayar da hodar Iblis.

Wasu majiyoyi kuwa sun bayyana cewa hukumar ta gayyaci Abba Kyari amma ya ki zuwa.

Kalli bidiyon:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

https://twitter.com/TheNationNews/status/1493226661847961601?s=20&t=dWg6uyaHXLWl9hpEC4E4_w

NDLEA na neman DCP Abba Kyari ruwa a jallo bisa zargin safarar kwayoyi

Kara karanta wannan

Karya ta kare: Abin da mutane ke cewa da NDLEA ta zargi Abba Kyari da safarar kwayoyi

Mun kawo muku rahoton cewa hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta ayyana jami'in dan sanda shugaban rundunar IRT da aka dakatar, DCP Abba Kyari cikin wadanda take nema ruwa a jallo bisa zargin safarar miyagun kwayoyi.

Hukumar NDLEA ta ce bincike ya nuna cewa Kyari mamba ne na wata kungiyar harkallar miyagun kwayoyi da ke hada-hadarta a fadin duniya.

Kakakin hukumar ya bayyana haka ne a wata zantawa da manema labarai a ranar Litinin, kamar yadda Legit.ng Hausa ta samo daga NDLEA.

A sanarwar da ta iso mu, NDLEA ta ce tana zargin Abba Kyari da yin harkallar hodar iblis da nauyinta ya kai kilo 25.

Hukumar ta kuma nuna damuwa kan cewa, ta yi mamakin yadda wadanda ya kamata su za su tsawatar amma su ake samu dumu-dumu a cikin miyagun laifuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel