Idan mu ka tafi yajin-aiki, za a garkame jami’o’i kenan sai illa Masha Allahu - Kungiyar ASUU

Idan mu ka tafi yajin-aiki, za a garkame jami’o’i kenan sai illa Masha Allahu - Kungiyar ASUU

  • Kungiyar ASUU ta na barazanar cewa idan suka tafi wani sabon yajin-aikin, babu ranar dawowa
  • Shugaban ASUU na shiyyar Owerri, Uzo Onyebinama ya bayyana haka da ya zauna da ‘yan jarida
  • Uzo Onyebinama ya yi bayanin abin da ya sa malaman jami’a suke tunanin sake rufe makarantu

Anambra - Kungiyar ASUU ta malaman jami’a ta reshen Owerri, tayi barazanar garkame jami’o’i sai lokacin da Allah ya yi, idan suka sake shiga yajin aiki.

Jaridar Punch ta fitar da rahoto, inda aka ji kungiyar ta ASUU ta na cewa ba za ta bude makarantu ba har sai an cika masu duka alkawuran da gwamnati tayi.

A wani taron manema labarai da ASUU ta kira a jami’ar Nnamdi Azikiwe, Awka, jihar Anambra, ASUU ta nuna ta na daf da tafiya yajin da babu ranar dawowa.

Kara karanta wannan

Tsaro: Kungiyar Izala ta yi kira da Buhari ya tashi tsaye, jama’a kuma su dage da addu'a

Uzo Onyebinama yace hakurin kungiyar ASUU ne ya jawo gwamnatin tarayya tayi watsi da tulin yarjejeniyar da aka rattaba hannu a kai tun a shekarar 2009.

Wasu malamai sun yi watanni babu albashi

A cewar Uzo Onyebinama, akwai malaman jami’an da suke bin bashin albashi har na watanni 10.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kungiyar ASUU
Wata jami'ar kudi a Najeriya Hoto: www.myschoolgist.com
Asali: UGC

Mista Onyebinama, wanda shi ne shugaban ASUU na shiyyar Owerri ya yi wannan bayani ne a ranar Litinin, 13 ga watan Disamba, 2021 a jihar Anambra.

Shugabannin ASUU daga FUTO Owerri, jami’ar jihar Imo, jami’ar Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu da jami’ar gona da ke Umudike sun halarci taron.

Jawabin shugaban kungiyar ASUU, Uzo Onyebinama

“Yanzu haka da mu ke magana, gwamnati ba ta cika manyan alkawuran da ta yi ba, daga ciki har da biyan kudin habaka da jami’o’i da alawus din EAA.”

Kara karanta wannan

Farfesa Jega ya fallasa dabarun Alkalai, ya bayyana yadda suke samun kudin haram

“Gazawar gwamnati na dabbaka yarjejeniyar 2009 ya jawo ASUU za ta tafi yajin-aiki, kuma idan aka tafi, ba za a dawo ba sai an biya mana bukatunmu.”

- Uzo Onyebinama

A wani rahoton, shugaban ASUU na shiyyar Benin, Farfesa Fred Esumeh yace yajin-aikin da suke shirin zuwa ya zama dole ne domin su jawo hankalin gwamnati.

Wahala za ta karu a shekara mai zuwa?

Ministar kudi da kasafin tattalin arziki ta kasa, Zainab Ahmed, ta kyankyasa cewa gwamnatin tarayya za ta kara lafta haraji domin samun kudin-shiga a 2022.

Gwamnatin Najeriya za tayi hakan ne domin ta rage dogaro da abin da aka samu daga man fetur. Ministar ta bayyana wannan da ta je gaban 'yan majalisar wakilai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel