EFCC ta damke Yakubu Musa kan laifin damfarar Surukinsa kudi N3m

EFCC ta damke Yakubu Musa kan laifin damfarar Surukinsa kudi N3m

Hukumar hana almundahana da yaki da rashawa watau EFCC, a ranar Laraba ta gurfanar da wani matashi mai suna Yakubu Musa kan zargin damfara a jihar Kaduna.

Yakubu Musa ya gurfana ne gaban Alkali Darius Khobo na babbar kotun jihar Kaduna.

A bisa jawabin Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren, ya ce ana zargin Yakubu da karban kudi N3m hannun wani Thalmon Friday wanda surukinsa ne a 2014 da sunan zai saya masa fili a unguwar Mahuta, jihar Kaduna amma ya karkatar da kudi, babu kudi babu fili.

EFCC ta bayyana cewa:

"Kai Yakubu a 2014 a Kaduna kayi awon gaba da kudi N3, 000,000.00(Miliyan uku) daga wajen Thalmon Friday kuma wannan laifi ne bisa sashe na 308 na Penal Code, kuma sashe na 309 ya hukunta."

Kara karanta wannan

Mu hada kai don Tinubu ya zama Shugaban kasa, Gwamna Sanwo-Olu ga shugabannin APC

Yakubu Musa
EFCC ta damke Yakubu Musa kan laifin damfarar Surukinsa kudi N3m Hoto: EFCC
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yakubu ya musanta zargin da akayi masa.

Sakamakon haka Lauyansa, Haruna Magaji, ya bukaci kotu ta bada belin Yakubu.

Alkali bayan sauraren dukkan bangarorin biyu, ya bada beli a kudi N2,000,000 da kuma mutum daya da zai tsaya masa.

An dage zaman zuwa ranar 21 ga Maris, 2022 don fara shari'ar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel