Miyagun ‘Yan bindiga sun sake aukawa garin Zaria, sun yi gaba da mutane cikin dare
- Ana fuskantar rashin tsaro a bangaren Zariya da ke Arewacin jihar Kaduna
- A ‘yan kwanakin nan, ana yawan garkuwa da mutanen da ke zaune a jihar
- ‘Yan bindiga sun shiga Mil Goma bayan sun yi wa wani ma’aikaci barazana
A karshen makon da ya wuce ne Legit.ng Hausa ta samu rahoton cewa wasu ‘yan bindiga su ka sake duro wa garin Zaria da ke jihar Kaduna.
An sake kai hari a Kofar Gayan
Sahelian Times ta bayyana cewa wadannan miyagun mutane sun kai hari a Kofar Gayan Low Cost, sun fafata da ‘yan banga da jami’an tsaro.
Jaridar ta ce an yi wannan ta’adi ne a ranar 9 ga watan Yuli, 2021 bayan duhun dare ya bayyana.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun afka wasu unguwanni a Zaria, sun sace mutane
‘Yan sa-kai sun yi kokarin hana ‘yan bindigan yin barnar da su ka yi niyya, na dauke ‘ya ‘yan wani soja, Manjo Aliyu Zubairu da ke zaune a yankin.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa an yi kokarin a dauke ‘ya ‘ya biyu na wannan mutumi, amma daga baya an tsinci yaran ba tare da an tsere da su ba.
An bada sunan wadannan yara da Abdulrahman Aliyu Zubairu da kuma Abubakar Aliyu Zubairu.
An tsere da wasu Yara da Mahaifiyarsu
A daidai wannan lokaci kuma aka shiga unguwar Mil Goma da ke yankin Shika, a karamar hukumar Giwa da ke iyaka da Katsina daga Arewa.
KU KARANTA: An hallaka mutane fiye da 70, 000 a cikin shekaru 10 a Najeriya
A nan mun samu labarin an sace wata Baiwar Allah da ‘ya ‘yanta uku. Wannan mata ta na aiki ne da asibitin koyarwa na Ahmadu Bello da ke garin Shika.
A lokacin da ‘yan bindigan su ka kawo hari da kimanin karfe 10:00 na dare, mai gidan wannan mata ba ya nan, ya na wurin aiki a Dutsinma, Katsina.
‘Yan bindigan sun fasa gidan, su ka dauke mutane hudu, su ka jefa su a cikin mota kafin 'yan gari su iya neman agajin jami’an tsaron da ke kewaye da su.
Wani mazaunin garin ya sha da kyar, da ya yi ido-hudu da 'yan bindigan da ya fito cikin daren. A baya 'yan bindigan sun yi barazanar kama wani a yankin.
A jiya aka ji 'yan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin Kajuru, Alhasan Adamu tare da wasu daga cikin iyalansa a wani hari da aka kai masa a ranar Asabar.
An yi gaba da baraken da matansa uku, jikokinsa biyu, hadimansa uku da wasu mutum biyar.
Asali: Legit.ng