'Dan Sarauniya: Lauya ya bayyana dalilin da yasa ƴan sanda suka kama tsohon kwamishinan Ganduje

'Dan Sarauniya: Lauya ya bayyana dalilin da yasa ƴan sanda suka kama tsohon kwamishinan Ganduje

  • Lauya ya bayyana dalilin ya sa yan sanda suka kama tsohon Kwamishinan Ayyuka na Kano, Mu'azu Magaji
  • Lauya ya ce ana zargin Mu'azu Magaji da ɓata suna da cin zarafin Gwamna Ganduje ne ta hanyar wallafa wani hoto a dandalin sada zumunta
  • Hoton na nuni da cewa gwamnan na Kano ba mutumin kirki bane domin yana aikata baɗala da wata mata da aka haska fuskar ta a hoton

Jihar Kano - Wani lauya ya danganta kama tsohon Kwamishinan Ayyuka a jihar, Mu'azu Magaji, da zargin wallafa hoto na ɓata suna da ya yi a dandalin sada zumunta.

Lauyan ya bayyana hakan ne a kotun majistare da ke zamanta a Nomansland a Kano inda aka gurfanar da Magaji, rahoton Daily Trust.

Yan sanda sun gayyaci tsohon Kwamishinan, Mu'azu Magaji, bayan karar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya shigar a kan tsohon kwamishinansa da ya sauya ya zama mai sukarsa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Ɗan Kwamishiniyar Ganduje a jihar Kano ya ɓace

'Dan Sarauniya: Lauya ya bayyana dalilin da yasa ƴan sanda suka kama tsohon kwamishinan Ganduje
Lauyan Mu'azu Magaji ya bayyana dalilin da yasa yan sanda suka kama shi. Hoto: Daily Trust
Asali: Twitter

An zargin Magaji da tada zaune tsaye, cin fuska da ɓata suna da gangan.

Rashin amsa gayyata yasa muka kama Magaji, Yan sanda

Daily Trust ta rahoto cewa an kama shi ne a Abuja bayan an yi hira da shi a wata shirin siyasa na Trust TV, a daren ranar Alhamis.

Yan sanda sun tabbatar da kama shi ta bakin kakakin yan sanda Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, inda ya ce an shigar da korafi a kansa ne.

Ya ce rashin amsa gayyatar da suka dade suna yi wa tsohon Kwamishinan yasa aka kama shi.

Sai dai ranar Juma'a, an gano cewa an kai Magaji kotun Majistare da ke Nomansland bisa korafin da gwamnan ya yi.

Ganduje ya yi korafi game wallafa hotunan bata sunansa da Magaji ya yi

Kara karanta wannan

'Karin bayani: 'Yan sanda sun cafke tsohon Kwamishinan Ayyuka na Kano, Mu'azu Magaji a Abuja

A cikin takardar korafin da gwamnan ya aike, an shaida wa kotu cewa Magaji ya wallafa wani hoto da ke nuna wanda muke karewa (Ganduje) a matsayin mutum mara tarbiyya da tsohon Allah da ke aikata baɗala da wata mata wanda aka haska fuskar ta a hoton.'

Lauyan gwamnan, Adekunle Taiye Falola, ya ƙara da cewa, "wanda ake zargin ya baza hoton a shafukan sada zumunta da dama, a wani yunkuri na ɓata wa gwamnan Jihar Kano suna da mutunci da kimarsa a matsayin ma'aikacin gwamnati kuma dan siyasa a Najeriya."

Amma lauyan Magaji ya ce wanda ya ke karewa ba zai iya amsa tuhumar da ake masa ba saboda ya kurmance sakamakon yadda yan sanda suka kama shi a Abuja.

Daga bisani, alkalin kotun ya bada umurnin a kai Magaji asibiti amma a tsare shi.

Ya dage cigaba sauraron karar zuwa ranar 31 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel