Masu daukar nauyin ta'addanci: Nan gaba kadan yan Najeriya za su barke da murna, Malami

Masu daukar nauyin ta'addanci: Nan gaba kadan yan Najeriya za su barke da murna, Malami

  • Ministan Shari'a ya roki yan Najeriya su ƙara hakuri game da fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci a Najeriya
  • Abubakar Malami ya tabbatar wa yan ƙasa cewa nan da yan makonni ma su zuwa za su yi farin ciki game da lamarin
  • A kwanakin baya gwamnatin shugaba Buhari ta sanar da cewa ta gano masu angiza wa yan ta'adda kuɗaɗe 96

Abuja - Ministan Shari'a kuma Antoni Janar na ƙasar nan (AGF), Abubakar Malami, ya roki yan Najeriya su ƙara hakuri game da fallasa sunayen masu ɗaukar nauyin ta'addanci.

Yayin da yake fira da Channels tv a cikin shirin 'Siyasa a yau' ranar Litinin, Malami ya tabbatar wa yan Najeriya cewa cikin yan makonni masu zuwa mutane za su sami madogara.

Kara karanta wannan

Karin Labari: Bayan dogon lokaci, Allah ya kuɓutar da dan uwan Jonathan daga hannun yan bindiga

Malami ya ce:

"Zaku yi farin ciki da matakan da muke ɗauka a gwamnatance nan da yan makonni masu zuwa. Bayan haka, zamu tuhumi waɗan nan mutanen, kuma mu gurfanar da su a gaban Kotu."
Abubakar Malami
Masu daukar nauyin ta'addanci: Nan gaba kadan yan Najeriya za su barke da murna, Malami Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Me gwamnatin Buhari take yi game da masu ɗaukar nauyin ta'addanci?

Ministan ya kuma ƙara da cewa gwamnati ta maida hankali wajen shirin hukunta masu hannu a lamarin ta hanyar doka, domin aiki ne da ba zai gamu lokaci ɗaya ba.

"Wajibi mu nemi kwararan hujjoji, daga nan kuma sai mu gurfanar da su kan zargin ta'addanci."
"Ba abin da zai kasance a ɓoye, kamar yadda ake kowace shari'a a bayyane, ba abin da zai ɓuya dangane da sunayen su, alaƙar su da ta'addanci, da kuma rawar da suka taka."

Malami ya tabbatar da cewa tuni gwamnati ta kudiri aniyar ganin doka ta yi aikinta ta hukunta masu laifin da ake zargi, kamar yadda Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ayyiriri: An sha shagali yayin da kwamishinan jiha ya biya sadaki, kayan ɗaki, aka ɗaura auren marayu 20

FG ta gano mutum 96

Kalaman Malami kan masu ɗaukar nauyin ta'addanci ya zo ne bayan gwamnatin tarayya ta ce ta gano wasu mutum 96 dake rura wutar ta'addanci da kuɗaɗen su.

Ministan labaru da al'adu, Alhaji Lai Muhammed, wanda ya faɗi haka ga manema labarai, yace sun gano mutanen na taimaka wa Boko Haram da yar uwarta ISWAP.

A wani labarin na daban kuma Ministan Sadarwa, Pantami ya faɗi babban abinda yan bindiga ke amfani da shi wajen ayyukan ta'addanci a Arewa

Minsitan sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami, yace yan bindiga na ribatar yawan faɗin kasa a jihohin arewa maso gabas wajen aikata ta'addanci.

Pantami yace hudu daga cikin jihohin Najeriya shida da suka fi faɗi duk suna yankin arewa maso gabas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel