Pantami ya faɗi babban abinda yan bindiga ke amfani da shi wajen ayyukan ta'addanci a Arewa

Pantami ya faɗi babban abinda yan bindiga ke amfani da shi wajen ayyukan ta'addanci a Arewa

  • Minsitan sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami, yace yan bindiga na ribatar yawan faɗin kasa a jihohin arewa maso gabas wajen aikata ta'addanci
  • Pantami yace hudu daga cikin jihohin Najeriya shida da suka fi faɗi duk suna yankin arewa maso gabas
  • A cewarsa, yan ta'adda na amfani da irin wuraren domin shirya kan su a maɓoyarsu, har su kaddamar da hari kan mutane

Abuja - Ministan harkokin sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, yace faɗin ƙasar da yankin arewa maso gabas ke da shi, yana taimaka wa wajen taɓarɓarewar tsaro a yankin.

The Cable ta rahoto cewa Pantami ya yi wannan furucin a wurin taron da hukumar raya Arewa maso gabas ta shirya, wanda ya gudana ranar Talata a Abuja.

Kara karanta wannan

Nasrun Minallah: Gwarazan Sojoji sun halaka dandazon mayakan ISWAP, sun tarwatsa sansanin su a Neja

Ministan yace hudu daga cikin jihohin Najeriya shida da suka fi faɗin ƙasa sun fito ne daga yankin Arewa Maso Gabas.

Ministan sadarwa, Isa Pantami
Pantami ya faɗi babban abinda yan bindiga ke amfani da shi wajen ayyukan ta'addanci a Arewa Hoto: @DrIsaPantami
Asali: Twitter

Ya kuma ƙara da cewa yan ta'adda na amfani da faɗin ƙasar dake akwai, wajen samun mafaka kuma su cigaba da aikata ta'addanci kan mutane.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Minista Pantami yace:

"Ina shawartan wannan hukuma, ɗaya daga cikin manyan kalubalen da arewa ta gabas ke fama da shi, shi ne yawan faɗin ƙasa."
"Ya kamata duk wani shiri da zamu yi aiki kansa mu tabbata mun yi cikakken tunanin yadda zamu fuskanci yawan faɗin ƙasa a yankin."
"A halin yanzu idan ka duba zaka ga huɗu daga cikin jihohin da suka fi faɗin ƙasa a Najeriya suna arewa maso gabas; Niger, Borno, Taraba, Kaduna, Bauchi da Yobe."

Wasu jihohin sun fi kasashe girma - Pantami

Kara karanta wannan

Sabuwar Matsala: Ɗaruruwan mambobin PDP a jihar da take mulki, sun sauya sheƙa zuwa APC

Pantami ya ce jihar Yobe kaɗai tana da girman 45,000 kmsq na faɗin ƙasa, wanda ya zarce ƙasashe 23 dake nahiyar Turai. Haka jihar Borno ta fi kasashe 30 a Turai girma.

"idan muka yi nazari zamu gano cewa zaman lafiya na tattare da yanayin faɗin ƙasa. Zaka sha mamaki meyasa Kano da Gombe suka fi zaman lafiya? Ina yaba wa shugabannin mu, Amma Kano da Gombe sun fi ko ina zaman lafiya a Arewa."
"Kuma sun fi kowace jiha a Arewa kankanta idan ana maganar faɗi. Yan ta'adda sun fi taruwa a wurin da yake da faɗi, inda za su ɓuya su shirya kan su ,domin kai hari."

A wani labarin na daban kuma Sheikh Pantami ya yi magana kan kisan Hanifa Abubakar, ya faɗi masifun da irin haka ke jefa al'umma

Ministan harkokin sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Pantami, ya bayyana darajar kananan yara yayin da yake martani kan kisan Hanifa Abubakar a Kano.

Kara karanta wannan

Kano: Sheikh Pantami ya yi magana kan kisan Hanifa Abubakar, ya faɗi masifun da irin haka ke jefa al'umma

Ministan, wanda babban malamin addinin Musulunci ne a Najeriya, ya ce mutane na cin albarkacin kananan yara wajen tausaya musu da Allah ke yi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel