Da Dumi-Dumi: Ɗan Sarauniya zai ƙara kwana a gidan gyaran hali saboda shari'ar Sheikh Abduljabbar

Da Dumi-Dumi: Ɗan Sarauniya zai ƙara kwana a gidan gyaran hali saboda shari'ar Sheikh Abduljabbar

  • Kotu ta ɗage sauraron karar tsohon kwamishinan ayyuka na Kano, Muazu Magaji saboda ta yi karo da shari'ar Sheikh Abduljabbar
  • A halin yanzun an ɗage ta Ɗan sarauniya zuwa 4 ga watan Fabrairu, 2022, yayin ta Malam Abduljabbar zata wakana 3 ga watan Fabrairu
  • Lauyan tsohon kwamishinan yace duba da dalilin da aka faɗa musu, ba yanda suka iya, sun rungumi kaddara

Kano - Tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Muazu Magaji, wanda aka fi sani da Ɗan Sarauniya, zai kara kwana ɗaya a gidan gyaran hali.

Daily Trust ta rahoto cewa hakan ta faru ne saboda ranar cigaba da shari'arsa ya ci karo da na Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, wanda ke gaban kotu kan zargin ɓatanci ga Annabi (SAW).

Kara karanta wannan

Za'a shirya Fim na musamman kan Hanifa Abubakar, yarinyar da aka kashe a Kano

Dan Sarauniya da Malam Abduljabbar
Da Dumi-Dumi: Ɗan Sarauniya zai ƙara kwana a gidan gyaran hali saboda shari'ar Sheikh Abduljabbar Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

A wata takarda, kwamishinan yan sanda na jihar Kano ya shaida wa alƙalin kotun Majistire mai lamba 58 dake Nomansland, matsalar da aka samu da shari'ar Magaji.

Wani sashin takardar yace:

"Alkalin kotun Majistire a Nomansland ya umarce ni na sanar da kai cewa ƙasancewar za'a cigaba da zaman shari'ar Sheikh Abduljabbar ranar 3 ga wata, wanda ya haɗu da shari'ar Magaji, wacce za'a yanke hukunci kan Beli.
"Saboda haka tun da jami'an tsaron ne za su kai Abduljabbar kotun musulunci dake K/Kudu, wannan Case na Ɗan Sarauniya an ɗage shi zuwa 4 ga watan Fabrairu, da misalin karfe 2:30 na rana."

Mun rungumi kaddara - Lauyan Ɗan Sarauniya

Da yake martani kan cigaban, Lauyan Muazu Magaji, Barista Garzali Datti Ahmed yace ba su yi tsammanin ɗage zaman shari'ar ba, amma sun karɓa da hannu biyu.

Kara karanta wannan

Kisan gilla: Bayan kisan Hanifa, wani Malami ya kashe Almajirinsa a jihar Kano

"Ba mu yi tsammani ba amma duba da dalilin da aka bayar wanda ya shafi tsaro, mun fahimta kuma mun amince da zuciya ɗaya."

Kotun Majistire dake zamanta a Nomansland ta umarci a tsare Muazu Magaji ne bayan an gurfanar da shi a gabanta.

A wani labarin na daban kuma Ɗaruruwan Ɗalibai a fusace sun toshe babbar Hanyar Legas-Abeokuta

Fusatattun daliban kwalejin fasaha a jihar Ogun, sun mamaye babbar hanyar Abeokuta zuwa Legas, sun hana kowa wuce wa.

Ɗaliban sun ɗauki wannan matakin na zanga-zanga ne domin nuna fushin su kan abin da yan sanda suka musu yayin da aka kai hari Hostel.

Asali: Legit.ng

Online view pixel