Da Dumi-Dumi: Fusatattun Ɗalibai sun toshe babbar hanyar Legas-Abeokuta saboda garkuwa da mutum biyu

Da Dumi-Dumi: Fusatattun Ɗalibai sun toshe babbar hanyar Legas-Abeokuta saboda garkuwa da mutum biyu

  • Fusatattun daliban kwalejin fasaha a jihar Ogun, sun mamaye babbar hanyar Abeokuta zuwa Legas, sun hana kowa wuce wa
  • Ɗaliban sun ɗauki wannan matakin na zanga-zanga ne domin nuna fushin su kan abin da yan sanda suka musu yayin da aka kai hari Hostel
  • Wasu yan bindiga sun kwashe awanni suna aikata ta'asa a wani hari da suka kai wa ɗaliban cikin dare

Lagos - Ɗaruruwan ɗaliban kwalejin fasaha ta D.S. Adegbenro ICT dake Itori, jihar Ogun, sun mamaye babbar hanyar Legas-Abeokuta ranar Laraba.

Premium Times ta rahoto cewa ɗaliban sun ɗauki wannan matakin ne bayan wasu tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da abokan karatun su mutum biyu.

Mahara sun sace ɗaliban ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare a Hostel ɗin su dake Afowowa, ƙaramar hukumar Ewekoro, jihar Ogun.

Kara karanta wannan

Za'a shirya Fim na musamman kan Hanifa Abubakar, yarinyar da aka kashe a Kano

Dalibai a Ogun sun fito zanga-zanga
Da Dumi-Dumi: Fusatattun Ɗalibai sun toshe babbar hanyar Legas-Abeokuta saboda garkuwa mutum biyu Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Meyasa ɗalibai suka toshe hanyar?

Fusatattun ɗaliban da suka fito zanga-zangan sun bayyana cewa sun fusata ne sabida ƙin daga kiran gaggawa da suka yi wa yan sanda yayin da yan ta'addan suka kawo harin.

Bugu da ƙari, ɗaliban sun yi ikirarin cewa maharan sun kwashe fiye da awanni hudu ba su bar Hostel ɗin ba.

Ɗaya daga cikin ɗaliban mai suna, Damilola, ya shaida wa manema labarai cewa saboda kwashe dogon lokaci babu wanda ya ƙalubalence su, yan bindigan sun tattara wayoyi, kwamfuta, kuɗi da sauran su, sun yi gaba da su.

Punch ta rahoto Ɗalibin yace:

"Mun kira lambar yan sanda ta gaggawa amma babu wanda ya ɗaga, daga baya kuma da suka ɗaga sai suka ce mana motarsu ta lalace."
"Daga ƙarshe da suka iso wurin, sai suka bukaci ɗalibai su jagorance su zuwa wurin yan bindigan. An harbi ɗalibi ɗaya a kafa, wasu kuma sun ji munanan raunuka. Dalilin mu kenan muka fito zanga-zanga kan hanya."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An jiyo ƙarar harbe-harben bindiga kusa da fadar shugaban ƙasar Guinea

Da farko ɗaliban sun mamaye ofishin yan sanda, amma yanzun sun haɗa babban cunkuson ababen hawa a hanyar da ta haɗa Abeokuta da Sango-Ota da Lagos.

Kazalika wani rahoto ya bayyana cewa da farko ɗaliban da suka fita zanga-zanga sun jefi yan sanda da duwatsu.

Da aka tuntuɓi kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, yace har yanzun bai samu bayani kan musabbabin zanga-zangan ba.

A wani labarin na daban kuma Jami'an tsaro sun aika wasu yan bindiga uku da suka addabi matafiya Lahira su haɗu da Allah

Yan sanda, sojoji da yan Bijilanti sun samu nasarar kashe yan bindiga uku daga cikin tawagar da ta addabi mutane a hanyar Benin-Auchi.

Yan bindigan sun kai hari kan hanyar ranar Talata amma jami'an tsaro suka kore su, suka sake fitowa yau Laraba aka kashe uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel