Ganduje ya gwangwaje jarumi Naburaska da mukami a gwamnatinsa

Ganduje ya gwangwaje jarumi Naburaska da mukami a gwamnatinsa

  • Gwamna Ganduje na jihar Kano ya gwangwaje jarumi Mustapha Naburaska da mukamin mai bayar da shawara kan farfaganda
  • Jarumi kuma mashiryin shiri, Falalu A. Dorayi ne ya wallafa a shafinsa na Instagram inda ya taya Naburaska murnar samun mukamin
  • A baya za a iya cewa alakar Naburaska da Ganduje ta yi tsami ganin yadda ya mayar da hankali wurin jam'iyyar adawa

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano, ya nada sanannen jarumin masana'antar Kannywood, Mustapha Naburaska, matsayin mai bada shawara a kan farfaganda.

Falalu A. Dorayi, jarumi kuma mashiryin fina-finai ne ya wallafa hakan a shafinsa na Instagram a ranar talatin ga wata wacce ta zama ranar Lahadi.

Ya taya jarumin murna tare da yi masa fatan alkhairi.

Kara karanta wannan

Na sanar da Atiku cewa ya tsufa kuma gajiye ya ke, ba zai iya shugabanci ba, Gwamnan Bauchi

Ganduje ya gwangwaje jaruman Kannywood 2 da mukamai a gwamnatinsa
Ganduje ya gwangwaje jaruman Kannywood 2 da mukamai a gwamnatinsa. Hoto daga @falalu_a_dorayi
Asali: Instagram

A cewar Dorayi, an gabatar da bikin nadin a lokacin da aka yi liyafar cin abincin dare wacce a aka gudanar a gidan gwamnatin Kano da maraicen ranar Asabar.

A baya dai, ana ganin Naburaska a matsayin wanda ba ya yin tafiyar Gwamna Ganduje, inda hatta wakoki da bidiyoyi ya sha daukar nauyi na dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP, gabanin zaben 2019 da ya gabata a Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Amma kuma ko kafin nadin, Naburaska ya ce a yanzu sun samu maslaha da gwamnan kuma ya ce ko a baya wasu miyagu ne suka shiga tsakaninsu domin hana ruwa gudu.

A wallafar Falalu Dorayi, ya ce:

“Muna godiya da wannan mukamai guda biyu. 1. Senior Special Assistant Kannywood (Malam Musa Khalid) 2. Special Adviser on Propaganda to the Governor (Mustapha Badamasi Naburaska).

Kara karanta wannan

Kisan Hanifa: Ganduje ya sake martani kan kisan Hanifa, ya ce dole ne a yi adalci

“Jiya [Asabar] bayan kammala dinner da Governor Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya mika mukamai guda biyu ga ’yan uwanmu.
“Daga yau duk wani mai bukata ko matsala tsakanin Kannywood da gwamnati to a nemi wadannan mutum biyu. Allah Ya taya ku riko, Ya baku ikon gamawa cikin amana da alkairi,” inji Falalu Dorayi.

Kano: Sadiya Haruna ta sha da kyar hannun Ƴan daba, sun yi yunƙurin watsa mata acid

A wani labari na daban, fitacciyar jaruma, Sayyada Sadiya Haruna, ta saki wani bidiyo inda ta koka kan wasu 'yan daba a birnin Kano sun yi yunkurin watsa mata acid a fuska a ranar Juma'a, 28 ga watan Janairu.

Cike da tashin hankali yayin da ta ke kuka tare da ihu ta yi bidiyon a cikin mota, inda wani matashi wanda ta kira da Besty ya ke jan ta.

A cewar Sadiya Haruna kamar yadda ta wallafa a shafin ta na Instagram, ta taso daga shagon ta inda ta ce wa kanin ta za ta biya kanti domin siyayya, shi ya karasa gida kafin ta iso.

Kara karanta wannan

Kisan gillan Hanifa: Ministan ilimi ya yabawa kokarin da gwamnatin Kano ke yi

Asali: Legit.ng

Online view pixel