Matatar Dangote da za a karasa a 2022 za ta dauki mutum 38, 000 aiki inji Shugaban AfDB
- Shugaban bankin cigaban Afrika, Dr. Akinwumi Adesina ya kai ziyara zuwa matatar Aliko Dangote
- Akinwumi Adesina ya yaba da wannan gagarumin aiki da babban mai kudin na Afrika ya dauko
- Tsohon Ministan gonan ya bayyana yadda matatar man da kamfanin takin za su taimakawa al’umma
Lagos - Dr. Akinwumi Adesina wanda shi ne shugaban babban bankin cigaban Afrika, ya kai ziyara zuwa matatar da Aliko Dangote yake ginawa a Legas.
A wannan ziyara ta ganewa ido, Dr. Akinwumi Adesina ya ga irin namijin aikin da kamfanin na Aliko Dangote yake yi domin samar da matatar tace danyen mai.
Da yake jawabi a shafinsa na Twitter, Akinwumi Adesina ya ce ya je ya ganewa kansa aikin da Dangote ya dauko, ya ce attajirin zai taimakawa kasashen Afrika.
A ranar Litinin 23 ga watan Junairu 2022, shugaban bankin na AfDB ya ce Dangote ya cancanci jinjina na kafa kamfanin da zai ba mutane hanyar samun abinci.
“Na yi farin cikin kai ziyara zuwa kayatacciyar matatar Dangote wanda duk Duniya ake ji da ita, tare da mai dakina da kuma Femi Otedola.”
"Duk lokacin da attajiran nan suka hada-kai, su na yin abubuwan ban al'ajabi. Najeriya ta na alfahari da su." - inji @Akin_Adesina a Twitter.
Mutane za su samu aiki
“Dangote Refinery and Petrochemical Industrial Zone kadai zai dauki mutane 38, 000 aiki; mutanen waje 11, 000 da ‘kuma Yan Najeriya 27, 000.”
“Za a ga tasirin samar da kamfanoni. Matasa da-dama za su samu ayyuka masu kyau. Mu cigaba da kokari wajen samar da kamfanoni a Afrika.”
"Kamfanin takin Dangote zai iya samar da ton miliyan uku na takin Urea. Wannan ne zai zama kamfanin takin zamani na biyu a girma a Duniya."
Adesina yake cewa bankin nahiyar na African Development Bank yana alfahari da gudumuwar da ya ba kamfanin Dangote Group wajen taimakawa Afrika.
“Aliko Dangote ‘dan kasuwa ne mai hangen nesa. Ya kamata a yabawa duk wanda ya yi irin abin da ya yi a nan…na ga kamfanin da zai bunkasa Afrika.”
- Akinwumi Adesina
Mai kamfanin BUA ya yi gaba
A farkon watan Junairun nan ne aka ji cewa dukiyar Abdulsamad Rabiu ta karu da $1.9b, Attajirin ya doke kusan kowa a sahun masu kudin Najeriya face Aliko Dangote.
Abdul Samad Rabiu ya mallaki sama da Dala biliyan 7, kusan Naira tiriliyan 3 ya ba baya kenan.
Asali: Legit.ng