Tun da an ki yarda a kara farashin mai, NNPC ta bukaci a bata N3tr kudin tallafi: Ministar Kudi

Tun da an ki yarda a kara farashin mai, NNPC ta bukaci a bata N3tr kudin tallafi: Ministar Kudi

  • Ministar kudin Najeriya ta bayyana adadin kudin da kamfanin NNPC ta bukata na kudin tallafin mai
  • Wannan ya biyo bayan dakatad da shirin kara farashin mai da gwamnatin tarayya tayi ranar Litinin
  • A ranar Laraba, farashin danyen mai ya tashi $90/ganga a kasuwar duniya, karon farko tun hawan Buhari mulki

Abuja - Kamfanin man feturin Najeriya (NNPC) ta bukaci kudi N3 trillion daga wajen gwamnatin tarayya matsayin kudin tallafin man fetur na 2022 tun da an fasa kara farashin mai.

Ministar Kudi, Zainab Ahmed, ta bayyana hakan ga manema labarai ranar Laraba a fadar Shugaban kasa bayan zaman majalisar zartaswa FEC.

Ta bayyana cewa maimakon N470 billion da aka ware na kudin tallafin Junairu zuwa Yuni, yanzu za'a biya karin N2.557 trillion saboda farashin mai ya tashi a kasuwar duniya.

Kara karanta wannan

Sabbin bayanai 4 game da Dangote da baku sani ba: Zai iya kashe N415m kullum na tsawon shekaru 40

Tace:

"Mun gabatar da bukatar karin kudi don bisa kudin tallafin mai dake cikin kasafin kudin 2022."
"Kamfanin man feturin Najeriya (NNPC) ta bukaci N3trillion daga wajen ma'aikatarmu na kudin tallafin man 2022. Hakan na nufin cewa zamuyi karin N2.557 trillion...wanda ke nufin N270 billion a wata."

Ministar Kudi
Tun da an ki yarda a kara farashin mai, NNPC ta bukaci a bata N3tr kudin tallafi: Ministar Kudi Hoto: NNPC
Asali: Twitter

A ranar Litinin, Gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin cire tallafin man fetur har sai baba ta gani.

Zainab Ahmed, ministar kudi, kasafi da tsarin kasa, ta sanar da hakan a wani taro da aka yi a majalisar dattawan kasar nan a Abuja a ranar Litinin.

Shugaban majalisar dattawan, Ahmed Lawan tare da karamin ministan man fetur, Timipre Sylva gami da manajan daraktan NNPC, Mele Kyari, duk sun halarci taron.

Kara karanta wannan

Tun da an ki yarda a kara farashin mai, zamu cigaba da cin bashi kenan: Fadar Shugaban kasa

Tun da an ki yarda a kara farashin mai, zamu cigaba da cin bashi kenan: Fadar Shugaban kasa

Najeriya zata ciyo basussukan kudi sakamakon dakatad da shirin kara farashin man fetur ta hanyar cire tallafin mai, fadar shugaban kasa ta bayyana ranar Laraba.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya bayyana hakan a hirar da yayi a tashar ChannelsTV.

A cewarsa, ko yan Najeriya sun so ko sun ki, dole a nemo kudi ta wani hanya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel