Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Borno za ta ƙwace ofisoshin UN guda 7 saboda kauce wa biyan haraji

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Borno za ta ƙwace ofisoshin UN guda 7 saboda kauce wa biyan haraji

  • Hukumar tattara kudaden shiga na Jihar Borno, BO-IRS, ta ce za ta kwace wasu ofisoshi mallakar Majalisar Dinkin Duniya a Maiduguri
  • Mohammed Alkali, shugaban BO-IRS ne ya bayyana hakan yana mai cewa hukumomin suna kauce wa biyan haraji ne tun Janairun 2021
  • Alkali ya ce duk da cewa an dauke wa kungiyoyin bada agaji biyan haraji akwai wasu rukunin harajin da ya kamata su biya wa ma'aikatansu da 'yan kwangila

Maiduguri - Gwamnatin Jihar Borno, a ranar Laraba ta ce za ta fara kwace kadarori guda bakwai mallakar hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da ke jihar saboda kauce wa biyan haraji, Daily Trust ta ruwaito.

Mohammed Alkali, Shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jihar Borno, BO-IRS, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a ranar Laraba a Maiduguri.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu ta bada umarnin kamo tsohuwar Minista ko ina aka ganta

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin Borno za ta kwace kadarorin UN saboda kauce wa biyan haraji
Gwamnatin Borno za ta kwace kadarorin UN saboda kauce wa biyan haraji. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce kadarorin da za a kwace sun hada da na World Health Organisation(WHO), World Food Programme(WFP), United Nations High Commission for Refugees(UNHCR), United Nations International Children Emergency Fund (UNICEF).

Sauran sun hada da na United Nations Office for the Coordination of Humanitarian Affairs (OCHA), Food and Agricultural Organisation(FAO), da United Nations Development Programme (UNDP) da ke ofisoshins a Maiduguri.

Kalamansa:

"Ya kamata a sani cewa galibi an dauke wa hukumomin nan biyan haraji daga kudaden da suke ayyuka da shi. Amma, dokar income tax, CAP P8 na tarayyar Najeriya ta 2004 ta wajabta musu biyan gwamnatin jiha abin da ake kira PAYE (Paye As You Earn) da Withholding Tax (WHT) domin ma'aikatansu da wadanda suka dauka matsayin yan kwangila.
"Sai dai tun daga Janairun 2021, ba su biya ba kuma an yi kokarin ganin sun biya din amma hakan ya ci tura, hakan yasa BO-IRS ta basu notis na kwana 30 idan ya cika ba su biya ba za a kwace gine-ginensu a ranar 24 ga watan Fabrairun 2022 kamar yadda aka ambata a baya."

Kara karanta wannan

AFCON 21: Sanata ba zai ci abinci ba, da martanin jama’a bayan yin waje da Najeriya

"Wannan hukumar za ta yi amfani da ikon da doka ya bata domin kwace kadarorin hukumomin da abin ya shafa."

Babagana Zulum: Ba ni da niyyar fito wa takara a zaɓen 2023

A wani labarin, Gwamna Babagana Zulum na Jihar Borno ya ce baya sa ran neman wata mukamin siyasa a shekarar 2023, Daily Trust ta ruwaito.

Akwai rade-radin cewa gwamnan yana neman yin takarar kujerar mataimakin shugaban kasa a Najeriya.

Amma, da ya ke magana wurin taron tattaunawa karo na 19 da Daily Trust ta shirya a ranar Alhamis a Abuja, ya ce bai taba fatan zai zama gwamna ba ma.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel