Hotunan Fani-Kayode da wasu mutum 3 da EFCC ta sake gurfanarwa kan damfarar N1.5bn

Hotunan Fani-Kayode da wasu mutum 3 da EFCC ta sake gurfanarwa kan damfarar N1.5bn

  • Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta sake gurfanar da tsohon minista, Femi Fani-Kayode
  • An sake gurfanar da shi tare da tsohuwar ministar kudi, Nnenadi Esther Usman, Yusuf Danjuma, tsohon shugaban ALGON da wani kamfani
  • Ana zarginsu da laifuka 17 da suka hada da hada kai wurin aiwatar da cuta tare da handame kudi har N1.5 biliyan kuma suka boye su ba bisa ka'ida ba

Ikoyi, Legas - Hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati, a ranar Litinin, 24 ga watan Janairun 2022 ta sake gurfanar da tsohuwar ministar kudi, Nnenadi Esther Usman da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode kan damfarar wasu makuden kudade.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Kotu ta bada umarnin kamo tsohuwar Minista ko ina aka ganta

A tare da su akwai Yusuf Danjuma, tsohon shugaban ALGON da kuma wani kamfani mai suna Joint-Trust Dimensions Nigeria Limited.

Hotunan Fani-Kayode da wasu mutum 3 da EFCC ta sake gurfanarwa kan damfarar N1.5bn
Hotunan Fani-Kayode da wasu mutum 3 da EFCC ta sake gurfanarwa kan damfarar N1.5bn. Hoto daga Economic and Financial Crime Commission
Asali: Facebook

Ana zargin su da laifuka 17 da suka hada da hadin kai wurin yin cuta da kuma adana kudi ba bisa ka'ida ba da suka kai naira biliyan daya da rabi.

Mai shari'a Daniel Osiagor na babban kotun tarayya da ke zama a Ikoyi ta jihar Legas ne ke kan shari'ar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jami'an hukumar EFCC sun damke tsohon minista Fani-Kayode

A wani labari na daban, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya shiga hannun hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta kasa (EFCC) a jihar Legas.

Punch ta rahoto cewa tsohon ministan na karkashin binciken hukumar ne bisa zargin amfani da jabun takardu da kuma magudi.

Femi Fani-Kayode, wanda aka fi sani da FFK a takaice, ya sake komawa jam'iyyar APC mai mulki a watan Satumba, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Watanni bayan dakatar da ita, Hadiza Bala Usman ta ga shugaba Buhari

Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da cewa jami'ai sun taso keyar FFK, amma yaki yin karin haske kan zargin da ake masa.

Da aka tambaye shi kan labarin kame tsohon ministan, Uwujaren yace: "Eh, ina tsammanin wani abu kamar haka ya faru," amma bai ƙara cikakken bayani kan zargin da ake masa ba."

FFK ya jima suna takun saƙa da hukumar EFCC na tsawon lokaci, kuma ta taɓa tsare shi na tsawon kwanaki 67 a shekarar 2016, tare da tsohuwar ministan kudi, Nnenadi Usman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel