Rikici ya yi rikici, ta kai an kashe wani Basarake, an babbaka abokansa har lahira a Ogun

Rikici ya yi rikici, ta kai an kashe wani Basarake, an babbaka abokansa har lahira a Ogun

  • Wasu ‘yan iskan gari da ba a san su wanene ba sun shiga karamar hukumar Ewekoro, sun kashe Sarki
  • Rahotanni sun ce an hallaka Mai martaba Oba Ayinde Odetola a daren yau tare da wasu abokansa
  • Rikici a kan wanda zai mulki kasar Alagado tsakanin mutanen Ake da Owu ne ya jawo wannan ta’adi

Ogun - A ranar Litinin 24 ga watan Junairu 2022, musiba ta aukawa karamar hukumar Ewekoro a jihar Ogun, inda aka kashe Basaraken yankin a garin.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Talatar nan cewa an hallaka Mai martaba Alagodo na kasar Agodo a garin Ewekoro, Oba Ayinde Odetola a yau.

Kawo yanzu da ake fitar da wannan labarin, ba a san su wanene su ka kashe Oba Ayinde Odetola.

Kara karanta wannan

Hotuna: Bayan kashe 'yan uwan sarki, 'yan bindiga sun tayar da bam a coci a Taraba

Manema labarai sun ji cewa bayan Mai martaba Ayinde Odetola da aka kashe, wadannan miyagun mutane sun babbaka wasu mutane uku a Ewekoro.

Ana zargin cewa wadannan mutane uku da aka yi wa kisan gilla, abokan Marigayi Ayinde Odetola ne. Jaridar The Naton ta tabbatar da wannan rahoto.

Basarake
Marigayi Oba Ayinde Odetola Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Me ya jawo wannan?

Rikicin sarautar gargajiya ne ya jawo wannan mummunan ta’adi. An dade ana rigima tsakanin mutanen Ake da Owu a kan wanene zai karbi sarautar Alagodo.

Sarkin da aka kashe ya fito ne daga cikin mutanen Ake a kasar Egba. Jama’a su na ganin mutumin Ake ba zai iya mulkar Owu da sun fi yawan jama'a ba.

A wani kaulin an ji cewa ba da dadewa ba aka samu an yi irin wannan kisan gilla a kasar Agodo inda wasu miyagun suka hallaka wani ‘danuwan Oba Otedola.

Kara karanta wannan

'Yan sanda da mafarauta sun hallaka 'yan bindiga, sun ceto wasu mutane a Adamawa

An kashe abokan Sarki

Da kimanin karfe 11:00 na daren yau aka kashe Oba Odetola tare da wasu abokansa uku a lokacin da suka shigo garin, su na dawowa daga wata tafiya da suka yi.

Rahoton na Daily Trust ya ce a halin yanzu mutane duk sun tsere daga kauyen bayan abin da ya faru. Wata ‘yaruwar marigayin ta shaidawa ‘yan jarida wannan dazu.

Mai magana da yawun bakin ‘yan sanda na Ogun, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce wasu jami'ai sun isa domin binciken abin da ya faru.

An daure masu walda

A jiya ake jin cewa Alkali ya zartar da hukuncin dauri ga masu walda da aka samu da satar kudin da aka aiko cikin asusun kungiyar domin karfafawa masu sana’ar.

Gwamnatin jihar Edo ta aiko da kudin ‘yan waldar, amma shugabannin kungiyarsu suka yi sama da wadannan miliyoyi. EFCC tayi nasarar aika su gidan yari a Benin.

Kara karanta wannan

Shirme ne: ‘Yan Twitter da Facebook sun yi kaca-kaca da Dalar shinkafar da aka yi a Abuja

Asali: Legit.ng

Online view pixel