Yanka makogwaron dalibi: Gwamnatin Borno ta bude shafin bincike

Yanka makogwaron dalibi: Gwamnatin Borno ta bude shafin bincike

  • Gwamnatin jihar Borno ta kaddamar da bincike a kan lamarin yanka makogwaron wani dalibin kwalejin El-Kanemi, Jibril Sadi Mato, da wani babban dalibi ya yi
  • Ma'aikatar ilimi ta jihar ta kafa kwamitin mutum biyar domin gudanar da binciken tare da kawo mata rahoto cikin mako daya
  • Mun dai ji cewa babban dalibin ya yi amfani da reza wurin yankar makogwaron Sadi wanda ya kasance dalibin karamin aji bayan sabani ya shiga tsakaninsu

Borno - Gwamnatin jihar Borno ta ma'aikatar ilimi ta kafa kwamitin mutum biyar domin bincike kan lamarin da ya yi sanadiyar yanka makogwaron wani dalibin kwalejin El-Kanemi, Jibril Sadi Mato, da wani babban dalibi ya yi.

Leadership ta rahoto cewa Kwamishinan ilimi na jihar Borno, Lawan Abba Wakilbe, wanda ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki, ya ce ya umurci sakatarensa da ya gaggauta kafa kwamiti don bincike.

Yanka makogwaron dalibi: Gwamnatin Borno ta bude shafin bincike
Yanka makogwaron dalibi: Gwamnatin Borno ta bude shafin bincike Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

A wata wasika zuwa ga shugaban kwamitin wanda shine sakataren ma'aikatar ilimi, Alhaji Sadiq Kadafur, dauke da sa hannun sakataren din-din-din na ma'aikatar, Mohammed Mustapha Abatcha, an umurci kwamitin da ya yi bincike.

Sannan an umurci kwamitin da ya gano musababbin lamarin da kuma bayar da shawara kan hanyoyin hana sake faruwar hakan.

An ba kwamitin, wanda ya hada da wakilin kwamishinan yan sanda, wakilin DSS, wakilin kwamandan NSCDC da daraktar tabbatar da inganci, ma'aikatar ilimi, Hajiya Hadiza Nasiru Wali, mako guda domin gabatar da rahotonsa ga kwamishinan ilimi na jihar, rahoton Daily Trust.

Borno: Ɗalibin sakandare ya keta makogwaron ɗalibin ƙaramin aji da reza don ya sa shi aiki ya ƙi yi

Mun ji a baya cewa Umar Goni, dalibin da ke babbar aji a makarantar su yana hannun jami’an rundunar ‘yan sanda bayan yunkurin halaka wani dalibin na karamin aji da ya yi a makarantar su, Daily Trust ta ruwaito.

An samu bayanai akan yadda ya yi amfani da reza wurin yankar makogwaron Jibrin Sadi Ramadan, daya daga cikin daliban kananun aji, bayan wani karamin rikici ya shiga tsakanin su.

Wakilin Daily Trust ya tattaro bayanai akan yadda lamarin ya faru a bayan dakunan kwanan daliban da ke Kwalejin El-Kanemi mai zaman kanta da ke Maiduguri cikin Jihar Borno, ranar Laraba da dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel