Gwamnan Arewa ya gafartawa mutum 49 da aka yanke wa hukuncin kisa a jiharsa

Gwamnan Arewa ya gafartawa mutum 49 da aka yanke wa hukuncin kisa a jiharsa

  • Gwamna Ortom na jihar Benuwai, ya yafe wa wasu mutum 50, mafi yawan su, suna jirar a zartar musu da hukuncin kisa ne a gidan Yari
  • Mutum 49 daga ciki suna kan hanyar zartar da hukuncin kisa, yayin da ɗaya kuma aka rage masa tsawon zamansa a gidan Yari
  • Akanta Janar kuma kwamishinan shari'a, Mista Gusa, yace ba duka mutanen ne yan asalin jihar Benuwai ba

Benue - Gwamnan jihar Benuwai dake arewacin Najeriya, Samuel Ortom, ya yafe wa mutum 50 dake zaune a gidan gyaran hali, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Mutum 49 daga cikin waɗan da lamarin ya shafa, suna jiran zartar da hukuncin kisan da aka yanke musu ne, yayin da mutum ɗaya aka rage masa wa'adin zaman sa a gidan kaso.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sake kai mummunan harin rashin imani jihar Neja, sun halaka dandazon mutane

Kwamishinan shari'a kuma Antoni Janar na jihar, Michael Gusa, shine ya tabbatar da haka yayin da yake zantawa da manema labarai a Makurdi.

Gwamnan Benuwai, Samuel Ortom
Gwamnan Arewa ya gafartawa mutum 49 da aka yanke wa hukuncin kisa a jiharsa Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yace gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne bayan shawarin da majalisar shari'a ta bayar, kuma matakin yafiyar ya dace da sashi na 212 a kwansutushin.

Yadda yafiyar ta shafi mutum 50

Kwamishinan ya bayyana cewa mutum 34 daga cikin waɗan aka yafe wa, suna jiran zartar da hukuncin kisa ne a gidan gyaran halin dake Jos.

Kazalika, yace wasu mutum 15, waɗan da aka yanke wa hukuncin kisa, sun samu canjin hukunci zuwa shafe ragowar rayuwarsu a gidan Yari.

Yayin da ragowar mutum ɗaya, aka rage wa'adin hukuncin da aka yanke masa na shekara 21 zuwa shekara 15 a gidan gyaran hali.

Kara karanta wannan

Dubun wasu gawurtattun yan leƙen asirin yan bindiga ya cika a Abuja

Vanguard ta rahoto kwamishina yace:

"Wasu daga cikin mutanen, sun ɗaukaka ƙara kan hukuncin da aka yanke musu amma ba su samu nasara ba."

Shin duka mutanen yan jihar Benue ne?

Mista Gusa, yace wasu daga cikin mutanen da lamarin yafiyar ya shafa yan asalin jihar Benuwai ne, yayin da wasu kuma yan wasu jihohin ne amma suka aikata laifi a jihar.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnan ya amince da matakin ne bayan samun amincewa daga gidan Yarin Jos da Sokoto, inda mutanen ke zaman jiran tsammani.

A wani labarin kuma Shugaban hukumar INEC, Farfesa Yakubu, ya bayyana babbar barazanar da ka iya hana zaben 2023

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu, ya bayyana damuwarsa kan ƙaruwar matsalar tsaro yayin da zaben 2023 ke ƙaratowa.

Yace matsalar tsaro babbar barazana ce kuma abun damuwa, amm duk da haka hukumarsa na iya bakin kokarinta tare da haɗin kan hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Yan bindiga sun bindige Basarake a jihar Arewa har lahira a cikin gidansa

Asali: Legit.ng

Online view pixel