Daura ta zama Landan: An yi kwana 30, wuta ba ta dauke ko sau 1 a mahaifar Buhari ba

Daura ta zama Landan: An yi kwana 30, wuta ba ta dauke ko sau 1 a mahaifar Buhari ba

  • A garin Daura da ke Arewacin jihar Katsina, an yi kwanaki 30 ba tare da an dauke masu wuta ba
  • Mazauna birnin sun dauki wata guda kenan a jere, ba su wutar lantarki ta dauke ko sau daya ba
  • Ana ganin garin ya na samun wutar ne saboda nan ne mahaifar Mai girma Muhammadu Buhari

Katsina - Rahotanni daga Katsina Post sun bayyana cewa an yi kwanaki 30 ba a dauke wutar lantarki ko sau daya a garin Daura, a jihar Katsina ba.

A ranar Talata, 18 ga watan Junairu, 2022 jaridar Katsina Post ta fitar da rahoto cewa an yi akalla wata guda ba a ga kiftawar wuta a garin na Daura ba.

Ba kasafai aka saba ganin an dauki tsawon lokaci ba tare da an ga daukewar wuta a Najeriya ba.

Kara karanta wannan

Sanatocin jihar Katsina 2 sun yi watanni 25 a Abuja, ba su kawo korafi ko shawara 1 ba

Sai dai yayin da aka shiga wannan sabuwar shekara ta 2022, sai aka ji cewa kwanaki 30 aka shafe ba tare da wuta ta dauke a cikin tsakiyar birnin ba.

Abin da hakan yake nufi, tun daga watan Disamban shekarar da ta wuce har zuwa yau, ko sau daya mutanen garin na Daura ba su zauna a cikin duhu ba.

FEC a Daura
Shugaba Buhari yana aiki daga Daura Hoto: von.gov.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutane su na more wuta

Jaridar ta samu wannan labari ne daga majiyoyinta da ke zaune a wannan tsohon gari. Masana tarihi su na cewa garin Daura ce cibiyar Hausawa a Duniya.

A halin yanzu mutane su na cewa wuta ta gyaru a Najeriya, amma wasu na ganin al’ummar Daura su na cin albarkacin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne.

Wasu na ganin lantarkin ya yawaita ne a sakamakon wasu gyare-gyare da aka yi kwanan nan.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga sun yi shigar soji, sun dauke ‘yan biki, sun bukaci a biya fansar Naira Miliyan 60

Mu na samun wuta yanzu

Legit.ng Hausa ta tuntubi wasu mazauna garin Katsina inda suka tabbatar da cewa su ma su na shafe sama da sa’o’i 16 da wutar lantarki a kusan kullum.

Wani mazaunin birnin ya ce a lokacin sanyi irin yanzu, lantarki ta na wadatarsu, sai dai kuma a lokacin damina da zafi, ana dadewa ba a ga kyalawar wuta ba.

Yanzu ba kamar da ba

A shekarar 2018 an ji yadda wani yanki na garin ya dauki tsawon lokaci ba tare da sun ga duriyar wutar lantarki ba, hakan ya jawo matsala a lokacin da ake azumi.

A wancan lokaci, Hon. Nasiru Sani Zangon Daura wanda shi ya ke wakiltar Yankin Zangon Daura a Majalisar Tarayya ya nemi a san yadda za ayi, a gyara wutan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel