Mutanen Garin Daura sun yi kwana-da-kwanaki babu lantarki
Kwanaki mu ka ji cewa Majalisar Wakilan Tarayya ta koka da wahalar wutan lantarkin da ake fama da shi a Yankin Garin Daura a Jihar Katsina bayan da wata na’urar da ke bada wuta ta buga saboda karfin iska.
Honarabul Nasiru Sani Zangon Daura wanda shi ke wakiltar Yankin na Zangon Daura a Majalisar Tarayya ya nemi masu harkar wuta su gyara na’urar 138KV da ke raba wuta da ta lalace ganin yadda jama’a ke zama cikin duhu a Garin.
‘Dan Majalisar ya nemi Hukumar NERC da kuma TCN mai jawo wuta da kuma kamfanin raba wutar na Yankin Kano da kewaye KEDCO su yi maza su gyara wutan Garin. Iska ce dai tayi gyara a Yankin da Shugaban kasa Buhari ya fito.
KU KARANTA: Sakataren zaben APC na kasa yayi murabus
Majalisar Tarayyar ta kuma jawo hankalin Ma’aikatar wutan lantarki na Kasar tayi wani abu a Garin Daura da ke cikin Jihar Katsina. Rashin wutan dai ya sa jama’a ke shan wahala a Kauyukan Daura yayin da ake azumin Ramadan.
Nasiru Sani Zangon Daura ya koka da yadda mutanen sa ke sayen kankara da tsada domin yin buda-baki. Kwanaki dai an gyara wutan sai kuma kwatsam abin ya lalace. Kakakin Majalisa Yakubu Dogara ya nemi a dauki mataki.
Kun san cewa Gwamnatin Buhari tayi alkawarin cewa zuwa badi war haka wuta zai karu. Ana sa rai a samu karin 1000MW daga tashohin wutan da ke kasar a badi. Ministan lantarki ya fi kowa samun kaso mai tsoka a kasafin kudin bana
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng