Allahu Akbar: Malamin Musulunci Ya Rasu Watanni 2 da Yin Hasashen Zai Bar Duniya

Allahu Akbar: Malamin Musulunci Ya Rasu Watanni 2 da Yin Hasashen Zai Bar Duniya

  • A makon da ya gabata aka rasa babban malamin shi’ar nan, Hamza Muhammad Lawal Badikko
  • Sheikh Hamza Muhammad Lawal Badikko ya rasu ya bar mata daya da ‘ya ‘ya biyar a Kaduna
  • An yi jana’izar shehin malamin, kuma an birne shi a makabartar Bashama da ke garin Kaduna

Kaduna - Sheikh Hamza Muhammad Lawal Badikko, wanda babban malamin addinin musulunci ne a Najeriya, ya rasu a jihar Kaduna.

Jaridar Aminiya tace an yi jana’izar shehin malamin a gidansa da yake Unguwar Marafa a garin Kaduna, bayan nan kuma aka birne shi.

An birne malamin ne a cikin makoki da jimami a shahararriyar makabartar Musulman nan da ke kan titin Bashama, duk a Kaduna.

Kamar yadda muka samu labari, an rufe malamin ne da kimanin karfe 3:00 na ranar Juma’a, Hamza Lawal Badikko ya rasu ne a ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Manufofin Babban Bankin Kasa Akan Fitar Da Kudi Tauyewa 'Yan Nigeria Hakk'ine – Masanin Kudi, Muda Yusuf

Kwatsam Malam ya mutu

Wata majiya ta shaidawa jaridar malamin bai yi fama da wata rashin lafiya ba, kwatsam sai ga ajali yayi kira, yana da shekara 59 da haihuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dalibin malamin da aka tattauna da shi yace Sheikh Hamza Lawal ya kasance abin koyi a wurinsu, wanda ya yi amfani da rayuwarsa a karantarwa.

Sheikh Hamza Lawal ya bar mata daya da za tayi masa takaba, sun haifi ‘ya ‘ya biyar.

Hamza Muhammad Lawal Badikko
Sheikh Hamza Muhammad Lawal Hoto: Muhammad Sagir Bauchi
Asali: Facebook

Malam yace ya kusa mutuwa

Legit Hausa ta fahimci cewa a makonnin baya aka ji malamin ya na mai nuna ya kusa mutuwa, yace yana jin ba zai kara shekaru bakwai a raye ba.

Wani dalibin marigayin, Muhammad Sagir Bauchi, ya yi magana a dandalin Facebook yace watanni biyu da suka wuce Shehin yace zai mutu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari Ta Ceto ‘Yan Najeriya Daga Yunwa Inji Ministan Buhari

“Haka kurum nake gani, ban san dalili ba, haka kurum nake gani… Abin da nake da ba na ganin zan kai shekara 7, ba ina nufin sai na kai shekara 7 daga yanzu ba
Ina nufin daga yanzu da nake zaune a nan zuwa shekaru 7, ina ganin ba zan wuce ba. Zan iya mutuwa yanzu, zan iya mutuwa kowane lokaci daga yanzu zuwa shekara 7”

- Sheikh Hamza Muhammad Lawal Badikko

Muhammad Sagir Bauchi yace yau wannan magana ta zama gaskiya, yake cewa malamin ya koyar da su duk abin da ake bukata na ilmin musulunci.

Hamza Lawal ya bambanta da Zakzaky

Kuna da labari cewa Marigayin ya kasance mai bin mazhabar shi’a, kuma jagora ne a kungiyar Al-Thaqalayn wanda ta sha bam-bam da kungiyar IMN.

Sakataren na kungiyar Al-Thaqalayn ya taba rike mukami a IMN. Hamza Lawal babban malami ne mai dinbin ilmi, ya yi karatunsa gida da waje.

Kara karanta wannan

Jonathan Ya Bude Baki Ya Yi Magana Kan Takara a APC da Sake Neman Mulki

Asali: Legit.ng

Online view pixel