Miji da mata da suka shiga aikin dan sanda a rana daya, sun zama kwamishinoni a rana daya

Miji da mata da suka shiga aikin dan sanda a rana daya, sun zama kwamishinoni a rana daya

  • Mata da mijinta, Kehinde Longe da Yetunde Longe sun samu karin girma zuwa kwamishinonin yan sanda a rana daya
  • Kehinde da Yetunde sun shiga aikin dan sanda ne a rana daya, sun hadu a makarantar horas da jami'an yan sanda ta Wudil a Kano a 1990
  • A makarantar suka fara soyayya daga bisani kuma suka yi aure, ma'auratan sun yi ayyuka a wurare daban-daban a rundunar yan sandan ta Najeriya

Babban Sufeta na Yan sandan Najeriya, Usman Baba, a ranar Juma'a, ya saka wa Kehinde Longe da matarsa, Yetunde Longe anini a matsayin kwamishinonin 'yan sanda, The Nation ta ruwaito.

Ma'auratan suna daga cikin wadanda Hukumar Kula da Harkokin Yan sanda ta yi wa karin girma tare da wasu 15 zuwa kwamishinoni.

Miji da mata da suka shiga aikin dan sanda a rana daya, sun zama kwamishinoni a rana daya
IGP na yan sanda yayin karrama sabbin jami'an da aka yi wa karin girma. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Wani mutum ya shiga hannu yayin da ya kashe yaransa uku ya adana gawarwakinsu a cikin firinji

Da ya ke karanto bayani dangane da su, Mai magana da yawun yan sanda, CP Frank Mba ya ce matar da mijin ajin su daya kuma sun shiga aikin dan sandan ne a rana daya a Maris din 1990.

Takaitaccen bayani game da ma'auratan

Miji da mata da suka shiga aikin dan sanda a rana daya, sun zama kwamishinoni a rana daya
Kehinde Longe da matarsa Yetunde Longe da aka yi karin girma zuwa kwamishinonin yan sanda a rana daya. Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Sun hadu ne a kwallejin horas da jami'an yan sanda da ke Wudil, Jihar Kano.

A nan suka fara soyayya har daga bisani suka yi aure.

Sun yi aiki a wurare daban-daban a jihohin Najeriya.

Yetunde ta taba shugabantar sashin binciken manyan laifuka, SCIID, na Panti, Yaba, Legas, rahoton The Nation.

Yayin shugabancinta, an yaba mata bisa kokarin ganin ta sauya kallon da ake yi wa yan sanda, ta kuma tabbatar da gaskiya da amana, sannan ta yi kokarin ganin ba a tsare mutane ba tare da dalili ba.

A lokacin, an samu nasarori sosai na bincike da hukunta masu laifi bayan kai su kotu.

Kara karanta wannan

Kowa ya debo da zafi: Kotu ta yanke wa matashi dan shekara 35 hukuncin kisa a Ibadan

Shi kuma mijinta, Kehinde, yayin da ya ke mataimakin kwamishinan yan sanda, shine kwamanda na Area H a Legas.

Ya kuma taba rike mukamin DCP na sashin ayyuka a Jihar Oyo.

Sauran wadanda aka yi karin girma

IGPn ya kuma saka wa wasu manyan yan sandan 22 anini cikinsu akwai mataimakan babban sufeta, DIG, na yan sanda biyu.

DIGn biyu sune DIG Zaki Ahmed da DIG Johonson Babatunde Kokumo.

Yayin da aka yi wa DIG Zaki karin girma domin maye gurbin da babu kowa sakamakon murabus din DIG Tijjani Baba a ranar 6 ga watan Oktoban 2021, shi kuma DIG Kokumo zai maye gurbin da DIG David Oyebanji Folawiyo, wanda ya yi ritaya a Nuwamban 2021 ne ya bari.

Adadin wadanda aka yi wa karin girman ya hada da DIGs biyu, mataimakan sufetan yan sanda shida, AIGs na yan sanda da kwamishinonin yan sanda 16.

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan sanda sun shiga tsakani yayin da kwarto ya kashe mijin daduronsa

A wani labarin, kun ji wani matashi, Walter, ya yi tattakain mil 20 a ranar sa ta farko ta zuwa wurin aiki. Motar sa ta samu matsala ana gobe zai fara zuwa aikin hakan ya sa ya yanke wannan shawarar.

Kafin safiyar, ya yi kokarin tuntubar abokan sa amma babu alamar zai samu tallafi saboda ya sanar da su a kurarren lokaci kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.

Daga nan ne ya yanke shawarar fara tattaki tun karfe 12am don isa wurin aikin da wuri. Matashin bai bari rashin abin hawan ya dakatar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel