Daukar aiki: Bayan shekaru biyu ana jira, NSCDC ta gayyaci mutum 5000 a cikin miliyan 1.5

Daukar aiki: Bayan shekaru biyu ana jira, NSCDC ta gayyaci mutum 5000 a cikin miliyan 1.5

  • NSCDC ta kasa ta fitar da sunayen mutanen da za a dauka aikin da aka tallata tun a shekarar 2019
  • An dauki kusan shekara biyu mutane su na jiran Hukumar ta fitar da jerin sababbin ma’aikatan
  • A lokacin da aka tallata aikin a 2019, mutane 1, 477, 042 suka nema, amma a karshe aka zabi 5000

Abuja - Shekaru biyu da fara shirin daukar aikin jami’ai a hukumar NSCDC, a karshe an fito da sunayen mutane 5000 da za su iya samun guraben aikin.

Jaridar Vanguard ta fitar da rahoto cewa mutane 5000 aka zaba daga cikin mutum miliyan daya da rabi da suka nemi wannan aikin a lokacin da aka tallata.

A lokacin da aka bude kafar daukar aikin na hukumar NSCDC a shekarar 2019, mutum 1, 477, 042 suka nema, daga baya aka rage adadinsu zuwa 217, 000.

Kara karanta wannan

An yi girgiza a Gwamnatin Tarayya, Minista ya yi nadin mukamai a NAMA, NCAA da FAAN

A karshen 2020 kuma aka sake zaftare adadin masu neman aikin zuwa 53, 116. Daga baya aka bar mutane 6, 500 kacal, har a karshe aka bar adadin a 5, 000.

Da yake magana da ‘yan jarida a birnin tarayya Abuja, shugaban jami’an hukumar NSCDC na kasa, Dr. Ahmed Abubakar Audi ya bayyana inda aka kwana.

Daukar aiki
Jami'an NSCDC Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Shugaban hukumar ta NSCDC yace sai da hukumar JAMB ta yi wa masu neman aikin jarrabawa.

Audi ya zanta da manema labarai ne tare da sakatariyar ma’aikatar CDFICB mai kula da jami’an kwana-kwana, gandurobobi da NSCDC, Misis Aisha Rufai.

Aisha Rufai tace daga ranar 17 ga watan Junairun nan, duk wanda ya kawo zuwa wannan gaba a wajen neman aikin zai iya duba shafin domin ganin ko ya dace.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: EFCC ta gurfanar da ‘babban yaro’ Mompha, ana zargin ya saci Naira Biliyan 6

Audi yace za a fara shirye-shiryen ba wadanda suka samu aikin takardu a ranar 31 ga watan Junairu.

Shugaban na NSCDC ya ce duk wani mai neman aiki yana da ranar da za a duba takardunsa, don haka babu bukatar ayi cincinrindo a sakatariyar hukumar.

Sanata Ovie Omo-Agege a 2023

Kungiyar Enyen-Nyen Movement ta wasu matasa a jihar Delta, ta bukaci Sanata Ovie Omo-Agege ya fito takarar gwamna a zaben 2023 ko a maka shi a gaban kotu.

Wannan kungiya ta Enyen-Nyen Movement ta cin ma wannan matsaya ne bayan wani taron gaggawa da tayi a tsakiyar makon nan a garin Ughelli, jihar Delta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel