An yi girgiza a Gwamnatin Tarayya, Minista ya yi nadin mukamai a NAMA, NCAA da FAAN

An yi girgiza a Gwamnatin Tarayya, Minista ya yi nadin mukamai a NAMA, NCAA da FAAN

  • Gwamnatin tarayya ta amince da nadin Mathew Lawrence Pwajok a matsayin sabon darektan rikon-kwarya a NAMA.
  • Nadin na Mathew Lawrence Pwajok yana zuwa ne yayin da wa’adin shugaba mai-ci, Kyatfin Fola Akinkuotu ya zo karshe

A ranar 7 ga watan Junairu wa’adin Akinkuotu ya cika, don haka aka nada wanda zai jagoranci NAMA na rikon kwarya

Daily Trust ta ce Ministan harkokin jirgin sama, Hadi Sirika ya amince da wasu nadin mukamai.

Pwajok ya yi aiki a ma’aikatar NAMA, har ya kai matsayin Darektan gudanarwa kafin ya yi ritaya a Disamba. Shi ne zai jagoranci hukumar na rikon kwarya.

Ma’aikatar harkokin jiragen sama ta aika takarda mai lamba FMA/ PS/ APPT/ CEO/014/1/23 ga ma’aikatar NAMA, ana sanar da ita wannan nadi da aka yi.

Kara karanta wannan

Alao – Akala: Muhimman abubuwa 15 da ya dace a sani game da tsohon gwamnan Oyo

“Ina sanar da kai Minista ya amince da nadin darektan gudanarwa, Pwajok Mathew Lawrence, ya kula da ofishin MD/CEO kafin nadin shugaba na din-din-din.”
“Ana bukatar ku ba darektan duk goyon-baya da hadin-kan da yake bukata wajen kula da wannan ofis. Mai girma Minista ya na aiko maku da sakon gaisuwarsa.”

- A. D Muhammad (Ma'aikata)

Rahoton ya ce Musa Mai Sallau wanda ya dade a kan kujerar Darekta, da Alhaji Umar Farouk Ahmed za su cigaba da zama a matsayin darektoci a NAMA.

Hadi Sirika
Ministan jiragen sama, Sanata Hadi Sirika Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

Kujeru FAAN, NCAA da sauransu

A hukumar FAAN, an sake nada Anozie Hanarius a matsayin darektar kula da ma’aikata, Aboderin Adenike ta zarce a matsayin darektar kudi da gudanarwa.

Haka zalika an bar Abdulkadir Rafindadi da Kyaftin Yusuf Muye a kan mukaman da suke a kai.

Kara karanta wannan

Yanzu nan: EFCC ta gurfanar da ‘babban yaro’ Mompha, ana zargin ya saci Naira Biliyan 6

The Eagle ta ce an nada Alli Maina ya zama sabon darektan sashen fasaha. Shi kuma Gold Bridget Iwinose zai jagoranci sashen shari’a na ma’aikatar tarayyar kasar.

Darektocin da aka nada a NCAA su ne Adamu Wakili da Kyaftin Chris Najomo. Bahagio Agio, Odunowo Tayib, Sani Bilikisu, da Ajiboye Isiak sun rike matsayinsu.

A hukumar AIB, Dayyabu Danraka ya rike kujerarsa. Mohammed Wali, Salisu Auwal sun zama Darektoci, yayin da Kakangi Aliyu zai taimaka kan harkar shari’a.

Charles Anosike, Abdul Ahmed, Saad Bashie, Abba Mailabi Yusuf da Effiom Oku sun zama darektoci a NiMET,

Godwin Emefiele ya yi kasa

A ranar Laraba ne aka samu rahoto cewa an fitar da gwarazan gwamnonin bankunan Duniya, babu Godwin Emefiele na Najeriya a sahun goma na farko a Afrika.

A 2021, Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya zo na 15 a cikin takwarorinsa 26.

Asali: Legit.ng

Online view pixel