Yanzu nan: EFCC ta gurfanar da ‘babban yaro’ Mompha, ana zargin ya saci Naira Biliyan 6

Yanzu nan: EFCC ta gurfanar da ‘babban yaro’ Mompha, ana zargin ya saci Naira Biliyan 6

  • A yau da safe ne jami’an hukumar EFCC suka gabatar da Ismailia Mustapha bayan an kama shi
  • EFCC ta na tuhumar Mustapha (Mompha) da kamfanin Ismalob Global Investment Ltd da cin kudi
  • Wannan shahahararren tauraro mai zama a Dubai zai wanke kan shi a kotu na musamman a Ikeja

Lagos - Hukumar EFCC mai yaki da almundahana da rashin gaskiya, ta gurfanar da Mr. Ismailia Mustapha wanda aka fi sani da Mompha yau a kotu.

A wani rahoto da Legit.ng ta samu, an kai Ismailia Mustapha da kamfaninsa Ismalob Global Investment Limited kara ne a wani kotu da ke Legas.

Alkalin wannan kotu na musamman da ke zama a Ikeja, jihar Legas, Mai shari’a Mojisola Dada ne zai yi shari’a tsakanin EFCC da wadanda ake tuhuma.

Kara karanta wannan

Hotunan yadda ginin wurin Ibada ya hallaka mutane suna tsaka da bautar Allah

Kamar yadda hukumar EFCC ta bayyana a shafinta, lauyoyi sun gabatar da Mompha da Ismalob ne a gaban Alkali a ranar 12 ga watan Junairu, 2022.

“An gurfanar da Ismaila Mustapha (Mompha) da safiyar yau, 12 ga watan Junairu, 2022 bisa zargin satar kudi da amfani da dukiyar da aka samu daga aika-aika.”
“An gabatar da shi a gaban Alkali mai shari’a na kotun da ke sauraron laifuffuka na musamman mai zama a garin Ikeja, Legas.” - Hukumar EFCC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Babban yaro’ Mompha
Mompha a hannun EFCC Hoto: OfficialEFCC
Asali: Facebook

Wani laifi Mompha ya yi?

Lauyoyin EFCC sun ce wadanda ake zargi sun yi kutun-kutun, sun satowa wani Olayinka Jimoh da aka fi sani da Nappy Boy kudi ta haramtaciyyar hanya.

Rahoton The Nation yace kudin da aka wawura sun kunshi N5,998,884.653.18, N32m, N120m, da N15,960,000. Adadinsu duk ya haura Naira biliyan shida.

Kara karanta wannan

Kowa ya debo da zafi: Kotu ta yanke wa matashi dan shekara 35 hukuncin kisa a Ibadan

Kawo yanzu Legit.ng Hausa ba ta samu labarin yadda ta kaya da Mompha a kotu ba.

Punch tace a ranar Litinin aka bada sanarwar cewa jami’an EFCC na reshen jihar Legas su ka sake ram da Ismailia Mustapha, ana tuhumarsa da laifuffuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel