Da Dumi-Dumi: Shugaban karamar hukuma ya yanke jiki ya fadi, ya kwanta dama a Asibiti

Da Dumi-Dumi: Shugaban karamar hukuma ya yanke jiki ya fadi, ya kwanta dama a Asibiti

  • Wani zababben shugaban ƙaramar hukuma a jihar Nasarawa ya kwanta dama a Asibitin babban birnin tarayya Abuja
  • Emmanuel Leweh, ciyaman na ƙaramar hukumar Akwanga, ya rasu ne bayan ya yanke jiki ya faɗi jim kaɗan bayan fitowa daga taro
  • Mamba a majalisar dokokin jihar Nasarawa, Samuel Tsebe, ya tabbatar da rasuwar yayan nasa da yammacin Alhamis

Nasarawa - Shugaban ƙaramar hukumar Akwanga, dake jihar Nasarawa, a arewacin Najeriya, Emmanuel Leweh, ya rigamu gidan gaskiya.

Wata majiya, da ta tattauna da jaridar Daily Trust, tace mamacin ya gudanar da wani taro da mambobin gwamnatinsa a Sakatariyar ƙaramar hukumar Akwanga, ranar Litinin.

A cewar majiyar da muka samu, marigayin ya yanke jiki ya faɗi a cikin Sakateriyar yankinsa, Akwanga, jim kaɗan bayan fitowa daga ganawar.

Kara karanta wannan

FG ta rantsar da kwamitin zartarwa na hukumar yaki da rashawa, EFCC

Jihar Nasarawa
Da Dumi-Dumi: Shugaban karamar hukumar ya yanke jiki ya fadi, ya kwanta dama a Asibiti Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Mista Leweh, wanda ya kwashe watanni uku kacal a ofishin ciyaman na Akwanga, ya mutu ne a wani Asibitin kuɗi dake babban birnin tarayya Abuja, ranar Alhamis.

Ɗan uwansa ya tabbatar da lamarin

Wani mamba a majalisar dokokin jihar Nasarawa, Mista Samuel Tsebe, ya tabbatar da mutuwar shugaban ƙaramar hukumar ga manema labarai.

Yace zababben ciyaman ɗin Akwanga, wanda yake ɗan uwansa na jini, ya rasu ne bayan fama da wata gajeruwar rashin Lafiya da yammacin Alhamis.

Honorabul Tsebe yace:

"Na rasa yayana, (Honorabul Emmanuel Joseph Leweh, zaɓaɓɓen shugaban ƙaramar hukumar Akwanga), ya rasu ne da yammacin nan bayan fama da gajeruwar rashin lafiya."

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun yi mummunar ɓarna a babbar Sakateriyar jam'iyyar PDP

Wasu yan bindiga ɗauke da muggan makamai da ake zargin yan daban siyasa ne sun farmaki sakatariyar PDP reshen jihar Ekiti.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An damke wasu masu shigo da muggan makamai Najeriya daga kasar waje

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun yi raga-raga da kujeru, sun lalata fayil-fayin, sannan kuma suka farfasa gilasan kofofi da tagogi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel