Dubu ta cika: An damke masu shigo da muggan makamai Najeriya daga kasar waje

Dubu ta cika: An damke masu shigo da muggan makamai Najeriya daga kasar waje

  • Dubun wasu masu aikin fasakwaurin muggan makamai daga Jamhuriyar Nijar zuwa Najeriya ya cika, an cafke su
  • Jami'an tsaro a jihar Maradi dake jamhuriyar Nijar sun kame mutanen ne yayin da suke kokarin safarar wasu makamai zuwa Najeriya
  • Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Najeriya ke fama da ayyukan ta'addancin yak bindiga a arewacin ƙasar

Niger - Jami'an tsaro sun samu nasarar kame wasu masu aikin shigo da muggan makamai cikin kasa Najeriya daga makociyarta Nijar.

Jami'an da suka yi wannan bajinta na aiki ne a yankin Dakwaro, a jihar Maraɗi, dake Jamhuriyar Nijar, kamar yadda Aminiya Hausa ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa jami'an sun damke mutanen ne dumu-dumu, yayin da suke yunkurin safarar wasu makamai zuwa Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya sa ladan tsabar kudi miliyan N5m ga duk wanda ya fallasa yan bindiga a jiharsa

Muggan makamai
Dubu ta cika: An damke masu shigo da muggan makamai Najeriya daga kasar waje Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamnatin Maradi ta yaba wa jami'an

Bayan samun labarin abin da ya faru, gwamnan jihar Maradi, Shu’aibu Abubakar, ya garzaya yankin Dakwaro, inda aka kame mutanen, kuma ya jinjina wa jami'an bisa wannan nasara.

Gwamnan ya nuna jin daɗinsa da kuma rokon jami'an tsaron su cigaba da kokarin dakile ayyukan irin waɗan nan mutanen.

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta daɗe da ɗaukar tsauraran matakan yaƙi da kuma kokarin kawo ƙarshen masu fasakwaurin makamai zuwa wasu ƙasashe, musamman waɗan da ke maƙwaftaka da Nijar.

Wane mataki gwamnatin Nijar ke ɗauka?

Legit.ng Hausa ta gano cewa, a baya-bayan nan sai da gwamnatin Nijar ta tsare wasu ma'aikatan ta bisa zargin hannu a wannan aika-aika ta safarar makami ba bisa ƙa'ida ba da kuma haramtattun kwayoyi.

A ɗaya bangaren kuma, gwamnatin Najeriya na ta faɗi tashin magance shigo da makamai ba bisa ƙa'ida ba daga wasu ƙasashe dake maƙwaftaka.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta bayyana gwamnan da zata goyi baya ya gaji shugaba Buhari a 2023

A halin yanzun, Najeriya na fama ayyukan ta'addancin yan bindiga a wasu jihohin arewa maso yamma.

A wani labarin kuma Sojojin NAF sun ceto yan kasuwan da yan bindiga suka sace a hanyar Birnin Gwari-Kaduna

Rundunar sojin saman ƙasar nan (NAF), tace dakarunta na musamman sun kwato mutum 26 daga cikin yan kasuwan da mahara suka sace a hanyar Birnin Gwari-Kaduna.

Wannan na zuwa ne bayan wasu tsagerun yan bindiga sun sace yan kasuwa da dama a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel