Mutane sun zub da hawaye bayan ganin bidiyon babban sarkin Najeriya yana waƙa tare da iyalansa dab da zai rasu

Mutane sun zub da hawaye bayan ganin bidiyon babban sarkin Najeriya yana waƙa tare da iyalansa dab da zai rasu

  • Wani bidiyo ya nuna marigayi Olubadan, Saliu Adetunji, ya na kwasar nishadi tare da waka tare da iyalansa yayin da ya ke kwance bisa gadonsa
  • Marigayin basaraken ya dage ya na dariya a cikin bidiyon duk da yanayinsa ya nuna cewa a jigace ya ke kuma babu wani kuzari tare da shi
  • ‘Yan Najeriya da dama sun yi tsokaci karkashin bidiyon inda su ka dinga cewa alamu na nuna yadda ya kula da yaransa a lokacin da ya ke a raye

Wani bidiyo wanda Goldmyne ta wallafa a shafinta na Instagram ya nuna yadda marigayi Olubadan, Oba Saliu Adetunji, ya yi nishadi tare da iyalansa kafin ya rasu.

A cikin bidiyon wanda ya karya wa mutane da dama zuciya, an ga basaraken kwance a gado yayin da iyalansa suka zageye shi suna wakoki.

Kara karanta wannan

Ina fatan ninka yawan 'ya'ya na, Magidanci mai yara 9 da ke cikin tsananin talauci da rashi

Mutane sun zub da hawaye bayan ganin bidiyon basaraken Najeriya yana waƙa tare da iyalansa dab da zai rasu
Hawaye sun kwaranya bayan ganin bidiyon basaraken Najeriya yana waƙa tare da iyalansa dab da zai rasu. Hoto: @goldmyne
Asali: Instagram

Bidiyon wanda Goldmyne ya wallafa an ga yadda ya kasance tare da iyalansa lokacin yana gab da mutuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duk jikinsa babu karfi a lokacin amma yana cikin nishadi

Kamar yadda aka gan shi, ya cika da farin ciki kwarai yayin da ya ke wakar tare da iyalansa amma dai duk jikinsa babu wani kuzari.

Akwai inda suke yin wakar har ya tsayar da su don ya jagoranci wakar yayin da suke taya shi.

Da alamu duk iyalan nasa cike suke da farin ciki yayin da suke yin wakar. Duk da yadda ciwo ya sa ya yi yaushi, amma ya na ta dariya.

Kali bidiyon a kasa:

Lokacin rubuta rahotonnan, mutane fiye da dari sun je kasan bidiyon inda suka dinga tsokaci a karkashin shi.

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin tsokacin jama’a kamar haka:

Kara karanta wannan

Duniya kenan: Yadda aka kama wani mutum da ke cin hanjin 'yan adam a Zamfara

amala_geng ta ce:

“Ban san shi ba, amma ganin yadda ya ke tare da yaransa na fahimci komai. Don yanzu da ayyukansa da tarbiyyar da ya ba yaransa ne kadai za su cece shi, amma alamu na nuna ya yi musu tarbiyya mai kyau.”

miz_winger ta ce:

“Muna fatan Ubangiji ya ba mu lafiya har zuwa lokacin tsufar mu.”

lordnmb ya ce:

“Akwai lokacin da zai zo a rayuwar mutum wanda duk wani kudi ba zai yi masa amfani ba.”

am_fabrics_world ta ce:

“Allah sarki, baba ya fahimci ya kusa tafiya. Muna fatan ka samu hutu a kabarinka.”

owopompin ya ce:

“Wannan abin burgewa ne.. Ubangiji ya yafe masa ya sa aljannar firdaus ce makomarsa...ameen.”

re_arrange2901 ta ce:

“Baba ya ga mutuwa tun lokacin!!! Ubangiji ya sa ya huta.”

Matar Shahararren Tsohon Gwamnan Najeriya Ta Rasu a Asibiti a Amurka

A wani labarin, Njideka Ezeife, matar tsohon gwamnan jihar Anambra wanda kuma dattijo ne a kasa, Chief Chukwuemeka Ezeife ta riga mu gidan gaskiya.

Kara karanta wannan

Wayyo: Mai imani ya ci karo da jakar kudi, bai tafi da komai ba sai N1800 na auno masara

Njieka ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a wani asibiti da ke Amurka kamar yadda kungiyar dattawan Igbo ta sanar ta bakin sakatarenta Farfasa Charles Nwekeaku, The Sun ta ruwaito.

Nwekeaku ya ce ana sa ran tsohuwar matar gwamnan za ta dawo Najeriya ne a ranar Litinin, 13 ga watan Disamban 2021 amma kwatsam ta fara rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel