Hana Twitter: Najeriya ta yi asarar N546bn a cikin kwanaki 222, mafi girma na 2 a duniya

Hana Twitter: Najeriya ta yi asarar N546bn a cikin kwanaki 222, mafi girma na 2 a duniya

  • Dakatar da Twitter ya zo a matsayin babban raunin tattalin arziki ga mutane da yawa wadanda suka dogara da kafar ta yanar gizo don yin kasuwanci
  • Dakatarwar da ta dauki tsawon kwanaki 222 kimanin watanni bakwai an yi kiyasin cewa ta jawo asarar tattalin arzikin sama da N546bn
  • A cewar wani lissafin NetBlock asarar tattalin arzikin da aka samu a tsawon lokacin da aka dakatar da twitter shine na biyu mafi girma a duniya

A watanni bakwai da suka gabata, gwamnatin Najeriya ta dakatar da Twitter, lamarin da ya kai tafka asarar NN546.5bn a lissafin da ya fito daga NetBlocks, kamar yadda Guardian ta ruwaito.

A cewar kayan lissafin, Najeriya na tafka asarar N103.17m (kimanin dala 250,600) a duk sa'a a fannin tattalin arziki bisa dakatar da Twitter.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari ya ce akwai alheri da yawa a yarjejeniyar Twitter da Najeriya

'Yadda Najeriya ta yi asarar kudade daga rufe Twitter
Twitter: Najeriya ta yi asarar N546bn a cikin kwanaki 222 | Hoto: Buhari Sallau
Asali: UGC

Gwamnatin Najeriya ta sanar da dakatar da shafin na Twitter a ranar Asabar 5 ga watan Yuni, 2021, haramcin ya tsaya ne bayan shafe kwanaki 222, wato sa'o'i 5328 kafin a dage shi a ranar Alhamis 12 ga watan Janairun 2022.

Asarar da kasashe suka fuskanta sakamakon rufe shafukan intanet

Dadewar da aka yi na takunkumin Twitter na nufin Najeriya ce ta biyu bayan kasar Myanmar idan ana maganar asarar tattalin arzikin da kasashe ke fama da su sakamakon rufe shafukan intanet.

Kiyasin da aka yi a bayanan Netblock, wani rahoto na Top10VPN ya kiyasta cewa a cikin 2021, Myanmar da ke karkashin mulkin soja a halin yanzu ta yi asarar dala biliyan 2.8 a cikin 2021 mafi girman asarar kudi daga rufe kafar intanet.

Kara karanta wannan

FG ta bayyana sharudda 5 da ta gindaya wa Twitter kafin dage dokar haramci

Sai kuma dala biliyan 1.5 na Najeriya yayin da Indiya ke matsayi na uku da dala miliyan 582.8.

Habasha ($164.5m), da Sudan ($157.4m) su ma sun shiga jerin wadanda suka tafka asara.

Sauran kasashe 10 da ke saman teburin asara

  1. Uganda $109.7M
  2. Bangladesh $49.7M
  3. Burkina Faso $35.9M
  4. Cuba $33.1M
  5. Syria $28.7M

Sai dai, karamin ministan kwadago, Festus Keyamo, SAN, ya ce Najeriya za ta fi morewa da duk wasu sharuddan da ta gindayawa dandalin sada zumunta na Twitter a yanzu.

Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis bayan gwamnatin shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ta janye dakatarwar shafin Twitter bayan sama da watanni bakwai.

A cewar Kayemi:

“Ga wadanda suka fifita siyasa a kan kishin kasa kuma suka nuna rashin gaskiya a kan dakatarwar Twitter, yanzu za su iya ganin cewa tare da duk sharuddan FG da Twitter ya amince da su, Najeriya ta fi samun alheri. Na taya Najeriya murna."

Kara karanta wannan

Daga bisani, iyalan Shonekan sun bayyana abinda yayi sanadin mutuwarsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel