Daga bisani, iyalan Shonekan sun bayyana abinda yayi sanadin mutuwarsa

Daga bisani, iyalan Shonekan sun bayyana abinda yayi sanadin mutuwarsa

  • Ernest Shonekan, tsohon shugaban kasan Najeriya ya yi rasuwar "Allah da Annabi" kamar yadda iyalansa suka sanar
  • Majiya ta sanar da cewa, tsohon shugaban kasan ya yi wata biyu a asibitin Evercare da ke Lekki a Legas kafin ya koma ga Ubangiji
  • Adeboye Shonekan, dan marigayin shugaban kasan ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar

Chief Ernest Shonekan wanda ya jagoranci gwamnatin Najeriya ta rikon kwarya wanda gwamnatin Janar Ibrahim Babangida ta karba mulki daga hannunsa, ya rasu a sa'o'in farko na ranar Talata.

Shonekan ya rasu a wani asibitin Legas mai suna Evercare da ke Lekki yayin da ya ke da shekaru 85 sakamakon gajeriyar rashin lafiya, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Daga bisani, iyalan Shonekan sun bayyana abinda yayi sanadin mutuwarsa
Daga bisani, iyalan Shonekan sun bayyana abinda yayi sanadin mutuwarsa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Majiyoyi sun ce tsohon shugaban Najeriyar ya yi sama da wata biyu a asibiti kafin mutuwarsa daga bisani.

Kara karanta wannan

Abun bakin ciki: Jam’iyyar PDP ta yi babban rashi na wani tsohon shugabanta

Shi ne shugaban gwamnatin rikon kwarya na Najeriya tsakanin ranar 26 na watan Augusta zuwa 17 ga watan Nuwamba duk a shekarar 1993 lokacin da aka yi masa juyin mulki karkashin jagorancin Janar Sani Abacha.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai, iyalansa sun tabbatar da rasuwarsa a jiya inda suka ce Shonekan ya yi 'mutuwar Allah da Annabi'.

Adeboye Shonekan a wata takarda da ya fitar a madadin iyalan, ya ce za su saki karin bayani, Daily Trust ta ruwaito.

Takardar tace:

"Dukkan daukaka ta na ga Ubangiji, iyalan Shonekan suna sanar da rasuwar sarki, masoyin mijin Margaret, mahaifi nagari gare mu kuma tsohon shugaban kasa, Chief Ernest Adegunle Oladehinde Shonekan, Baba Sale na Egbaland.
"Ya rasu a safiyar yau salin alin yayin da yake da shekaru 85 a duniya. Iyalan za su sake sakin karin bayani lokacin da ya dace."

Kara karanta wannan

Najeriya ta yi rashi: Tsohon shugaban kasa a Najeriya Ernest Shonekan ya rasu

Marigayi Shonekan ya rasu ya bar matarsa Margaret da 'ya'ya hudu da suka hada da Korede Shonekan, Adeboye Shonekan, Kemi Shonekan da Yele Shonekan.

Tarihin Marigayi Shonekan wanda ya yi kwana 83 a mulki, Abacha ya yi masa juyin-mulki

A wani labari na daban, an haifi Ernest Shonekan ne a ranar 8 ga watan Mayu, 1936, ya rasu saura watanni hudu ya yi bikin cika shekaru 86 da haihuwa kenan a Duniya.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa an haifi Marigayin ne a garin Ogun, ya rike sarautar Abese na kasar Egba, kuma yana auren Margaret Shonekan.

Tsohon shugaban kasar na rikon kwarya ya yi karatun ilmin shari’a ne a jami’a. Bayan ya zama Lauya sai ya shiga harkar kasuwanci a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel