Shugaba Buhari ya bada umurnin rage tsayin tutar Najeriya sakamakon mutuwar Ernest Shonekan

Shugaba Buhari ya bada umurnin rage tsayin tutar Najeriya sakamakon mutuwar Ernest Shonekan

  • Shugaba Buhari ya bada umurnin rage tutar Najeriya na tsawon kwanaki uku bisa mutuwar Ernest Shonekan
  • Wannan umurni ya shafi dukkan ma'aikatu, ofishohi, makarantu da wuraren da akwai tutar Najeriya
  • Ernest Shonekan ya mulki Najeriya na yan watanni rikon kwarya bayan saukar Ibrahim Babangida

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar tsohon shugaban kasan rikon kwarya, Cif Ernest Shonekan wanda ya mutu ranar Talata, 11 ga Junairu, 2022.

Buhari ya bada umurnin rage tsayin tutar Najeriya a fadin tarayya saboda nuna jimamin mutuwar tsohon shugaban.

Ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

A cewarsa, za'a yi wannan na tsawon kwanaki uku.

Yace:

"Na nada umurnin rage tsayin tutar Najeriya zuwa rabi, daga ranar Laraba 12 zuwa Juma'a 14 ga Junairu, 2022, don girmama tsohon Shugaban rikon kwaryan Najeriya da ya mutu, Chief Ernest Shonekan, GCFR."

Kara karanta wannan

Daga bisani, iyalan Shonekan sun bayyana abinda yayi sanadin mutuwarsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaba Buhari ya bada umurnin rage tsayin tutar Najeriya sakamakon mutuwar Ernest Shonekan
Shugaba Buhari ya bada umurnin rage tsayin tutar Najeriya sakamakon mutuwar Ernest Shonekan
Asali: Facebook

Chief Ernest Shonekan wanda ya jagoranci gwamnatin Najeriya ta rikon kwarya wanda gwamnatin Janar Ibrahim Babangida ta karba mulki daga hannunsa, ya rasu a sa'o'in farko na ranar Talata.

Shonekan ya rasu a wani asibitin Legas mai suna Evercare da ke Lekki yayin da ya ke da shekaru 85 sakamakon gajeriyar rashin lafiya.

Majiyoyi sun ce tsohon shugaban Najeriyar ya yi sama da wata biyu a asibiti kafin mutuwarsa daga bisani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel