Doyin Salami: Abubuwa 12 da ya dace a sani game da masanin da zai ceto tattalin Najeriya

Doyin Salami: Abubuwa 12 da ya dace a sani game da masanin da zai ceto tattalin Najeriya

  • Abuja - A ranar Talata, 4 ga watan Junairu, 2021 aka ji cewa Muhammadu Buhari ya nada Dr. Doyin Salami a matsayin mai bada shawara kan harkar tattali
  • Hakan na zuwa ne bayan shugaban Najeriyar ya shafe shekaru kusan bakwai a kujera kuma saura masa kimanin shekara daya da rabi ya sauka daga mulki
  • Mun tattaro wasu bayanai da ya kamata masu karatu su sani game da Dr. Doyin Salami wanda ake sa ran zai farfado halin da kasar nan ta ke ciki nan da 2023

Haihuwa

1. Kamar yadda shafinsa na Wikipedia ya nuna, tace an haifi Doyin Salami ne a garin Ijebu-Ode, jihar Ogun a Afrilun 1963, yanzu ya na da shekaru 58 a Duniya.

Karatun boko

Kara karanta wannan

Bayan dogon jira, fim din 'Gidan Badamasi' zango na 4 zai shiga kasuwa nan kusa

2. Hadimin shugaban kasar ya yi digirinsa na PhD a Queen Mary College da ke jami’ar Landan. Salami ya yi digirin farko da na biyu a bangaren tattalin arziki.

Daga ina aka zakulo shi?

3. Wannan ne karon farko da Muhammadu Buhari zai nada cikakken mai ba shi shawara a kan harkar tattalin arziki tun da ya zama shugaban kasa a 2015.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

4. Kafin yanzu, Dr. Doyin Salami ne shugaban kwamitin PEAC mai ba Mai girma Muhammadu Buhari shawara a kan abin da ya shafi tattalin arziki a Najeriya.

Aikace-aikacen da ya yi

5. Salami masanin tattali ne, malamin makaranta, kuma mai bada shawara, ya na aiki a makarantar koyon kasuwanci ta Lagos Business School.

6. Dr. Salami yana aiki tare da wasu manyan kamfanoni da hukumomin Duniya irinsu DFID, majalisar UNIDO, USAID da kuma babban bankin Duniya.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Minista ya bayyana hanyar da Buhari zai bi wajen sakin Nnamdu Kanu

7. The Cable tace Salami shi ne babban manajan kamfanin Kainos Edge Consulting Limited. Bayan nan ya na cikin ‘ya ‘yan kungiyar AGSA ta Afrika.

Doyin Salami
Farfesa Doyin Salami / PEAC Hoto: businesspost.ng
Asali: UGC

Shiga gwamnati

8. Ya taba zama cikin kwamitin MPC na babban bankin CBN, sannan ya yi aiki a majalisar da ke ba gwamnatin tarayya shawara a kan harkar tattalin arziki.

9. Salami ya yi aiki da Ahmed Joda a kwamitin da ya yi aiki wajen mikawa Buhari ragamar mulki.

10. Haka zalika Salami ya na cikin shugabannin da ke kula da majalisar Nigerian Economic Summit Group.

Aikin da zai yi

11. Doyin Salami ne ake sa rai zai rika bibiyar halin da tattalin arzikin kasa ke ciki, ya rika ba shugaba Buhari shawarwarin matakai da tsare-tsaren da suka kamata.

12. Har ila yau, Dr. Salami ne zai bada shawarar manufofin da za su taimakawa gwamnatin Najeriya wajen samar da aikin yi, rage talauci da zaburar da tattalin kasa.

Kara karanta wannan

Dawo-dawo: Tsohon Shugaban kasa Jonathan ya yi zaman sirri da masu so ya koma kan mulki

Daliban Kwankwasiyya sun yi suna

Kun ji cewa wasu mutane uku da suka amfana da tsarin Kwankwasiyya na tura hazikan matasa zuwa makarantun kasashen waje sun yi suna yanzu a Duniyar kimiyya.

An rahoto cewa wadannan masana 'yan jihar Kano; Aliyu Isa Aliyu, Tukur Abdulkadir Sulaiman, da kuma Abdullahi Yusuf su na cikin masu binciken da ake ji da su a yau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel