Na yi iyakan kokarina, ban tsammanin yan Najeriya sun min godiya: Shugaba Buhari

Na yi iyakan kokarina, ban tsammanin yan Najeriya sun min godiya: Shugaba Buhari

  • Shugaba Buhari ya sake zantawa da yan jarida don amsa tambayoyin dake zukatan yan Najeriya
  • Shugaban kasan yace bai tsammanin yan Najeriya zasu yi masa godiya bisa namijin kokarin da yayi
  • Buhari ya bayyana irin ayyukan kwarai da ya yiwa Najeriya a tsawon rayuwarsa

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa bai tsammanin godiya daga wajen yan Najeriya idan wa'adinsa ya kare saboda ya riga ya yiwa Najeriya iyakan kokarinsa.

Buhari ya bayyana hakan ne a hirar da yayi da gidan talabijin NTA ranar Alhamis.

Yace:

"Na yi Gwamna, na yi Minista, kuma ina wa'adi na biyu matsayin Shugaban kasa. Saboda haka na ga dukkan tsare-tsaren, menene kuma ya rage zan yiwa kasar nan?"
"Na yi iyakan kokarina, kuma ina sa ran idan na tafi, yan Najeriya zasuyi waiwaye. Ba na tsammanin yan Najeriya su yi min godiya."

Kara karanta wannan

Buhari: Tsufa ya fara nuna wa a jiki na amma dai nagode wa Allah

Shugaba Buhari
Na yi iyakan kokarina, ban tsammanin yan Najeriya sun min godiya: Shugaba Buhari Hoto: Aso Villa
Asali: Twitter

Abinda nike son yan Najeriya su yi min

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana sa ran idan ya sauka daga mulki zasu fadi da kansu cewa ya yi iyakan kokarinsa.

Buhari yace:

"Abinda nike sa ran yan Najeriya suce shine mutumin nan ya yi iyakan kokarinsa."

Buhari ya bayyana cewa idan ya sauka daga mulki zai huta sosai saboda ya aikatu.

Don ka yi karatu bai zama dole ka samu aikin Gwamnati ba, Buhari ga Matasan Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi kira ga matasan Najeriya suyi amfani da ilmin da suka samu a makaranta da wayewa wajen inganta kawunansu sabanin dogaro kan aikin gwamnati.

"Na so idan suka je makaranta; suka yi kokari; suka samu digiri, kada suyi tunanin dole ne sai gwamnati ta basu aiki," ya bayyana.

Kara karanta wannan

Ina son yan Najeriya suce na yi iyakan kokari na, Shugaba Muhammadu Buhari

"Ka nemi ilimi ne saboda mai ilimi ya fi mara shi, ko wajen fahimtar matsalolin kai. Saboda haka ba a neman ilimi don gwamnati ta bada aiki ko kuma abinda turawan mulkin mallaka suka dasa mana a kai na cewa sai ka yi mota, ka yi gini, kana zuwa aiki karfe 8 ka dawo karfe 2."

Asali: Legit.ng

Online view pixel