Tsohon dan majalisa zai biya N4m kan yi wa wata mata tumɓur da cin zarafin ta

Tsohon dan majalisa zai biya N4m kan yi wa wata mata tumɓur da cin zarafin ta

  • Babbar kotu a Akwa Ibom ta umarci wani mutum da matarsa su biya wata mata naira miliyan 4 saboda yadda su ka yi mata tsirara
  • Har ila yau, mutumin, Uduak Nseobot da matarsa, Anieda za su kara biyan wata N200,000 don bayyana gaban kotu
  • Sai da Nseobot da matarsa su ka sace ta daga Uyo su ka wuce da ita karamar hukumar Ibiono Ibom da ke jihar, sannan su ka mata tumbur

Uyo, Akwa Ibom - Wata babbar kotu a Uyo da ke jihar Akwa Ibom ta bukaci wani dan majalisa da matarsa da su biya wata mata naira miliyan 4 saboda yi mata tsirara a gaban jama’a.

Dan majalisar mai suna Nseobot da matarsa, Aniedi za su kara biyan wata N200,000 ga matar saboda kudaden da ta kashe na yawon kotu, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Magidanci ya lakadawa budurwa dukan tsiya, ya umarci matansa su kashe ta a jihar Kano

Tsohon dan majalisa zai biya N4m kan yi wa wata mata tumɓur da cin zarafin ta
Tsohon dan majalisa zai biya N4m kan yi wa wata mata tumɓur da cin zarafin ta. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Nseobot, a watan Nuwamban 2018, sun sace matar, Iniubong Essien a Uyo, sannan suka zarce da ita karamar hukumar Ibiono Ibom da ke jihar, tafiyar mintuna 27 inda shi da matarsa su ka yi mata tsirara bisa zarginta da sace musu kudade.

A cewarsu, an watsa kudade ne a wurin bikinsu - abinda mutane da dama suke yi a bukukuwan Najeriya, Premium Times ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sai dai Essien ya sa aka shafa wa jikin ta gawayi sannan aka daura mata igiya a kugunta, sannan suka takura ta don ta yi rawa.

Lamarin ya auku ne lokacin Nseobot yana kansila a wata gunduma da ke karamar hukumar Ibiono Ibom.

Matar da suka ci zarafi, Ms Essien, kawa ce ga matar Nseobot kusan shekaru 10, kuma ta musanta satar kudin.

Alkalin, Edem Akpan, yayin yanke hukuncin a ranar Alhamis ya ce, abinda Mr Nseobot da matarsa suka yi bai dace ba.

Kara karanta wannan

Gombe: Mai adaidaita sahu ya yi garkuwa da kansa don ya samu N500,000 ya biya bashin da 'yar uwarsa ke binsa

Alkalin ya ce, lamarin da mutumin ya yi bai dace da halayyar ‘yan siyasan Najeriya ba saboda hakan rashin kare hakkin dan adam ne.

Wani lauya mazaunin Legas, Inibehe Effiong wanda ya maka kara akan tozarta hakkin bil Adama a maimakon Ms Essien, ya sanar da Premium Times cewa kotu ta wanke wacce yake karewa.

Wacce aka ci zarafi, Ms Essien bayyanawa Premium Times farin cikinta akan shari’ar inda tace ta ji dadin yadda ba su tsira ba daga aika-aikar da suka yi.

Mfon Ben shi ne lauyan da ya wakilci Ms Nseobot da matarsa a kotu. An yi kokarin kiransa don jin ta bakinsa amma abin ya ci tura.

Dan Najeriya ya maka MTN a kotu kan cire masa N50, an biya shi N5.5m diyya

A wani labari na daban, Wani dan Najeriya mai suna Emmanuel Anenih a watan Oktoban 2014, ya maka kamfanin sadarwa na MTN a gaban kotu kan cire masa naira hamsin da aka yi kuma aka saka masa wakar kira duk da bai bukata ba.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Wasu masu tone kabari su sace sassan jikin mamata sun shiga hannu

Kamar yadda shafin @naija_reporter suka ruwaito, bayan fafatawa da aka yi tsakanin Emmanuel na kamfanin MTN, ya samu galaba a shari'ar inda kotu ta umarci MTN da ta biya shi makuden kudi.

A yadda ta kaya a kotun, bayan da alkali ya tabbatar da samun shaidu gamsassu cewa an cutar da shi, an yankewa kamfanin sadarwa na MTN hukunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel