Ogbonna: Dalilan da suka sa Buhari yake tsoron sakin Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu

Ogbonna: Dalilan da suka sa Buhari yake tsoron sakin Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu

  • Saint Moses Ogbonna ya soki yadda Mazi Nnamdi Kanu yake fafutukarsa ta kafa kasar Biyafara
  • A cewar Saint Moses Ogbonna, Muhammadu Buhari zai ji tsoron fito da shugaban na kungiyar IPOB
  • ‘Dan gwagwarmayar yace tsoron shugaban kasar shi ne ko Nnamdi Kanu ya fito, kila ba zai tuba ba

Abuja - Fitaccen ‘dan gwargwamayar nan, Saint Moses Ogbonna yace Muhammadu Buhari zai ji tsoron fito da Mazi Nnamdi Kanu saboda bai da tabbas.

Moses Ogbonna yana ganin Mai girma shugaban kasa zai ji tsoron ya saki shugaban IPOB, Mazi Nnamdi Kanu domin tsoron zai iya komawa gidan jiya.

A wata hira da Saint Moses Ogbonna ya yi da Vanguard, da ta fito a ranar Alhamis, 6 ga watan Junairu, 2022 yace Buhari bai yarda Kanu zai tuba ba.

Kara karanta wannan

2023: Shugaba Buhari ya yi magana game da ‘Dan takarar da zai so ya gaje shi a karagar mulki

A hirar da aka yi da shi, ‘dan gwagwarmayar ya gargadi shugaban na kungiyar IPOB ya yi hattara.

Ogbonna ya hakikance za a iya shawo kan matsalar Nnamdi Kanu kamar yadda Muhammadu Buhari ya yi wa su Mbazuluike Amaechi alkawari a baya.

Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Hoto: AP
Asali: UGC

Za a iya yi wa Kanu afuwa

“Muhammadu Buhari ya na da karfin ikon da zai iya yi wa Mazi Nnamdi Kanu afuwa.”
“Amma shin shugaban kasa yana ganin Nnamdi Kanu ya yi nadama, zai canza halinsa idan an yi masa afuwa?”
“Ina tunanin ya kamata Kanu ya daina yi kamar babu yadda shugaban kasa ya iya, dole ya yi masa afuwa tun da ya na fafutukar Biyafara.”
“Tsoron Buhari shi ne idan aka yi wa Kanu afuwa, zai koma jeji ya cigaba da fafutukar da yake yi.” - Saint Moses Ogbonna.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Ba zan saki Nnamdi Kanu ba, ya kare kan shi a gaban kotu, Buhari

Inda Kanu ya yi kuskure a fafutukarsa

Mista Ogbonna ya fadawa jaridar cewa lamarin Nnamdi Kanu ya fi karfin siyasa, sha’ani ne na kabilanci, kuma Kanu ya yi kuskure da ya shigar rigar IPOB.

Haka zalika yace wani kuskure da Nnamdi Kanu yake yi a fafutukarsa shi ne ba ya tafiya da dattawa a gwagwarmayar IPOB, sannan ya na zagin manya.

Wannan rashin kunya na cikin abubuwan da suka canzawa Buhari ra'ayi, a cewar Ogbonna.

Ba zan sake shi ba - Buhari

Da aka yi hira da shi a makon nan, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce shugaban 'yan taware na kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya kare kansa a kotu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya lashe amansa bayan an ji kwanaki ya na nuna yiwuwar gwamnatinsa ta yi wa Kanu afuwa duk da maganarsa ta na kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel