‘Diyar tsohon Sarki Sanusi ta taya iyayenta murnar cika shekara 30 da aure da tsofaffin hotuna

‘Diyar tsohon Sarki Sanusi ta taya iyayenta murnar cika shekara 30 da aure da tsofaffin hotuna

  • Khadija Sanusi Lamido Sanusi ta yi addu’o’i domin taya iyayenta cika shekaru 30 da yin aure a Duniya
  • Yusrah Sanusi ta na cikin ‘ya ‘yan tsohon Sarkin Kano, Mai martaba Malam Muhammadu Sanusi II
  • Mahaifiyarta, Sadiyo Ado Bayero ce uwargidar Sanusi II, 'diya ce wajen Marigayi Sarki Ado Bayero

Lagos - Khadija Sanusi Lamido Sanusi wanda aka fi sani da Yusrah, ta yi magana yayin da iyayenta suka cika shekara 30 da auren junansu.

A shafin ta na Twitter mai suna KhadijaSanusi_, Khadija Sanusi Lamido Sanusi tayi wa iyayen na ta addu’ar murnar zagayowar ranar da suka yi aure.

Khadija Sanusi Lamido Sanusi wanda ta kira kanta da Lady Sanusi ta yabawa iyayen na su, ta kuma roki Allah ya karo masu shekaru na kaunar juna.

Kara karanta wannan

An daure ‘Dan Najeriya da yake aiki a asibitin kasar Amurka saboda laifin kwanciya da masu jinya

Ga wadanda ba su sani ba, Yusrah Sanusi na cikin ‘ya ‘yan mai martaba tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II da uwargida Sadiya Ado Bayero.

Maganar Khadija Sanusi Lamido a Twitter

“Ina taya murnar cika shekara 30 da auren Mama da Baba! Mun gode da ku ke kaunar junan ku kwarai da gaske.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Ina fatan Allah ya sa a kara yin wasu shekaru 30 nan gaba (Idan Allah ya so), cikin soyayya da kauna da fara’a.”
“Ina kaunarku har gobe. x” - Khadija Sanusi Lamido
Tsofaffin hotunan Sanusi
Sanusi II da Sadiya Ado Bayero a baya Hoto: Yusrah Sanusi
Asali: Twitter

Khalifa Muhammad Sanusi II ya je Ghana

Yayin da suke cika shekaru 30 da aure, Legit.ng Hausa ta ji cewa Khalifa Muhammad Sanusi Lamido II ya kai ziyara zuwa kasar Ghana a halin yanzu.

Muhammad Sanusi Lamido II ya jagoranci sallah a masallacin Sharubutu a garin Accra, Ghana.

Kara karanta wannan

Siyasa: Manyan rigingimun da suka aukawa jam’iyyun PDP da APC a shekarar 2021

Mutane su na ta maida amsoshi ga Khadija Sanusi Lamido, inda da yawa suke taya iyayen na ta murna, wasu kuma su na yabon tsohon Sarkin na Kano.

"Shi fa Sarki tun da ‘dan gayu ne."

- Danjummai Garba

"Ma sha Allah, Allah ya kara masu zaman lafiya da kwanciyar hankali."

- Dan Mama

"Ina taya iyayenki murnar zagayowar ranar aurensu. Allah ya cigaba da ba su kariya."

- Kabir Jibril

"Ma sha Allahu."

- Ahmad Rufai Bala

Iyalin Khalifa Sanusi II

Matan Khalifa Sanusi II hudu ne a Duniya; Hajiya Sadiya Ado Bayero ita ce Uwargida. Sai kuma Hajiya Maryam Sanusi da Sa'adatu Musatapha-Barkindo.

A ranar Lahadi 4 ga Watan Agusta, 2019, Sa'adatu Musatapha-Barkindo ta tare a gidan Sanusi II.

Asali: Legit.ng

Online view pixel