Bashir Tofa: Bayani a kan rayuwar Marigayin da hirar karshe da ya yi a kan mulkin Buhari

Bashir Tofa: Bayani a kan rayuwar Marigayin da hirar karshe da ya yi a kan mulkin Buhari

  • A ranar 3 ga watan Junairu, 2022, aka samu labarin rasuwar dattijon Arewa, Alhaji Bashir Othman Tofa
  • Legit.ng Hausa ta tattaro wasu daga cikin abubuwan da ya kamata a sani game da rayuwar Marigayin.
  • An haifi Marigayin a birnin Kano a shekarar 1947 kuma ya yi karatunsa ne a gida Najeriya da Birtaniya

1. Haihuwa

An haifi Bashir Othman Tofa a ranar 20 ga watan Yuni,1947 a birnin Kano. Iyayensa bare-bari ne da suka zo Kano.

2. Karatu

Marigayi Bashir Othman Tofa ya fara karatun firamare a makarantar Shahuci Junior Primary da ke Kano.

Daga nan ya karasa karatun firamaren na sa a makarantar City Senior Primary School duk a cikin birni.

A 1962 Tofa ya tafi makarantar Provincial College, Kano, ya kuma yi nasarar kammalawa a shekarar 1966.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bashir Tofa, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Zaɓen 1993, Ya Rasu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

3. Fita kasar waje

Tsakanin 1970 zuwa 1973, Tofa ya na Birtaniya, inda ya yi karatu a City of London College da ke Landan.

4. Aiki

A shekarar 1967 Marigayin ya samu aiki da kamfanin inshora na Royal Exchange Insurance company.

Bashir Tofa
Alhaji Bashir Othman Tofa Hoto: @hallirunazeer
Asali: Facebook

5. Siyasa

Tofa bai dade ya na aiki a kasar waje ba, bayan dawowarsa gida sai ya tsunduma cikin harkar siyasa.

A shekarar 1977 Bashir Tofa ya zama Kansila a Dawakin Tofa bayan an kirkiro kananan hukumomi.

Marigayi Tofa ya na cikin ‘yan majalisar da suka tsara kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1979.

Bayan aikin da suka yi a 1977, Tofa ya shiga jam’iyyar NPN da sojoji suka bada dama a dawo siyasa.

Tsakanin 1979 da 1983, Marigayin ya rike mukamai dabam-dabam a jam’iyyar NPN a reshen Kano da kasa.

Tofa ya taba zama Sakataren jam'iyyar NPN a reshen jihar Kano da sakataren kudin jam’iyyar na kasa.

Kara karanta wannan

Shekaru kadan bayan nada shi sarauta, fitaccen basarake ya riga mu gidan gaskiya

6. Takarar shugaban kasa

Shekaru kusa ngoma bayan an yi juyin-mulki, Tofa ya shiga daya daga cikin jam’iyyun da sojoji suka kafa

Alhaji Tofa ya nemi takarar shugaban kasa a jam’iyyar NRC bayan an hana wasu shiga takara a 1992

Jam’iyyar NRC ba tayi nasara ba, alkaluma sun nuna MKO Abiola na jam’iyyar SDP ya doke ta har a Kano.

7. Dattijon Arewa

Daga baya Attajirin ya ajiye harkar siyasa, ya cigaba da kasuwancisa da kuma kare Arewacin Najeriya.

Hirar karshe da Bashir Tofa

A wata hira da ya yi da BBC, Tofa ya koka cewa gwamnatin Buhari ba ta daukar shawara kan batun tsaro.

Wannan hira a 2020 na cikin maganar da aka yi da shi na karshe inda yace kokarin gwamnati mai-ci, bai isa ba.

Marigayin ya tabo zancen zanga-zanga da wasu matasa ke yi domin ankarar da shugaba Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel