Babu kanta: Makamai da harashin ‘Yan Sanda 178,459 sun bace a shekara daya inji AuGF

Babu kanta: Makamai da harashin ‘Yan Sanda 178,459 sun bace a shekara daya inji AuGF

  • Akalla bindigogi da sauran makamai 178, 459 ake lissafin sun bace daga hannun ‘yan sanda a 2019
  • Rahoton binciken da ofishin AuGF ya gudanar ya nuna an rasa inda makamai da yawa suka shiga
  • Sannan kuma ana zargin shugabannin rundunar ‘yan sandan Najeriya da badakalar kwangiloli

Abuja The Nation tace wani rahoto da babban mai binciken gwamnatin tarayya ya fitar, yace makamai iri-iri kusan 178, 459 sun bace daga rumbun ‘yan sanda.

Binciken da ofishin AuGF ya gudanar na shekarar 2019 ya nuna cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya ba su sanar da hukuma game da bacewar makaman ba.

Haka zalika binciken ya zargi shugabannin ‘yan sanda da kin bada bayani kan makamai da harsasun da suka tashi aiki ko wadanda ba za su iya aiki da kyau.

Kara karanta wannan

Aiki ga mai yin ka: El-Rufai ya sanar da mataki 1 tak na magance 'yan bindiga

Jaridar Vanguard tace hakan zai iya jawo a rika amfani da makamai ta hanyar da ba ta dace ba.

Wannan bayani da AuGF ya yi, ya na dauke ne a rahoton binciken da aka yi a kan duka ma’aikatu da kuma hukumomin gwamnatin tarayya a shafi na 383 zuwa 391.

IGP Usman Baba
Shugaban 'yan sanda, Alkali Usman Baba Hoto: punchng.com
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban mai binciken gwamnatin tarayya, Adolphus Aghughu ya sa hannu a binciken a watan Satumban 2021, kuma an aika rahoton zuwa ga akawun majalisar.

NPF sun saba dokar kasa

Wannan danyen aiki da rundunar ‘yan sandan Najeriya tayi, ya sabawa sakin layi na 2603 na dokokin tarayya. Hakan ya na iya zama barazana ga harkar tsaro.

A ka’ida idan bindigar ‘dan sanda ta bace, dole ayi gaggawar sanar da hukuma a cikin kwana uku.

An rasa AK-47 fiye da 80, 000

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sake farmakar jihar Kaduna, sun yi mummunan aika-aikata

Zuwa Disamban 2018, bindigogi da makaman ‘yan sanda da aka rahoto cewa sun bace sun kai 178,459. Daga cikin wannan adadi akwai bindigogin AK-47 88,078.

Sannan akwai kananan bindigogi 3,907 da aka rasa inda suka shiga zuwa Junairun 2020. Bayan haka akwai zargin badakalar kwangiloli da aka tafka a gidan NPF.

Dubun wata ja'ira ta cika a Kaduna

A makon nan ne ku ka ji cewa Dakarun IRT sun yi nasarar cafke wanda ke yi wa ‘Yan bindiga safarar ‘yan mata a jejin Galadimawa da ke garin Zaria, jihar Kaduna.

Mariya matar aure ce da ta hada wani ‘Dan bindiga mai suna 'Dan Inna da ‘yanuwanta da kuma yaran cikinta har biyu domin miyagun su rika lalata da su a cikin jeji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel