Jami’an tsaro sun damke matar auren da ta ke kai wa ‘Yan bindiga yaranta domin su yi lalata

Jami’an tsaro sun damke matar auren da ta ke kai wa ‘Yan bindiga yaranta domin su yi lalata

  • ‘Yan sanda masu binciken manyan laifuffuka sun kama matar da ta ke kai wa ‘Yan bindiga mata
  • Mariya matar aure ce da ta hada wani ‘Dan bindiga da ‘yanuwanta da kuma yaran cikinta har biyu
  • Wannan matar tace ta na kai yaran zuwa dajin Galadimawa domin ‘yan bindiga su yi amfani da su

Kaduna - Dakarun ‘yan sanda masu binciken manyan laifuffuka sun kama wata mata wanda ake zargi da taimakawa miyagun ‘yan bindiga da ‘yan mata a jeji.

An fahimci cewa wannan Baiwar Allah mai suna Mariya ta na kai wa ‘yan bindigan da suka addabi kewayen garin Zariya ‘yan mata domin su yi amfani da su.

Jaridar Aminiya ta samu zantawar da wannan mata tayi, inda ta bayyana irin ta’adin da ta ke yi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun sake farmakar jihar Kaduna, sun yi mummunan aika-aikata

Mariya matar aure ce da ke tare da mijinta a unguwar Hanwa-Zaria, karamar hukumar Sabon Gari, jihar Kaduna, ta na da alaka da wasu miyagun ‘yan bindiga.

Mariya tayi magana a bidiyo

A wani bidiyo mai sunan mintina uku, matar ta bayyana yadda take daukar ‘ya ‘yan ‘yanuwanta, ta kai su cikin jeji wajen miyagun da suke garkuwa da mutane.

Jaridar ta yi hira da ita bayan dakarun ’yan sandan da ke yaki da ’yan fashin daji da miyagun ’yan ta’adda sun cafke ta, inda ta fayyacewa Duniya danyen aikinta.

An kama Mariya
Mariya mutumiyar 'Dan Inna Hoto: aminiya.dailytrust.com
Asali: UGC

A cewar Mariya ta na shiga dajin Galadimawa domin kai wa wani ‘danuwanta (‘Dan-Inna), matan da zai yi fasikanci da su bayan ya nemi ta nema masa budurwa.

Yadda abin ya fara - Mariya

Kara karanta wannan

Ka tuna da alkawarin da ka dauka: 'Yan Arewa sun roki Buhari kada ya basu kunya a 2022

Lamarin ya fara ne bayan wannan mata ta ba wata budurwa mai suna Lawisa lambar wayar wani ‘Dan Inna, inda suka fara soyayya har suka hadu da juna a jeji.

Da farko ta ce ta ki yi wa ‘Dan Inna budurwa saboda ba aikin alheri yake yi ba. Amma daga baya sai ta bijirowa Lawisa da maganar, har abin ya kankama da kyau.

Bayan nan kuma sai ‘Dan Inna wanda ‘dan bindiga ne da ke zaune a dajin Galadimawa ya sadu da kanwar wannan matar aure da kuma wasu yaranta biyu da ta haifa.

Matar ta shaida mana da cewa ‘ya ‘yan na ta da kanwarta su na zuwa wajen gungun ‘Dan Inna, tace idan za su je dajin, sai an kira ‘Dan Inna domin ya shiga da su.

'Yan sanda sun yi kamu a Kano

Dazu aka ji cewa rundunar 'Yan sanda a jihar Kano sun bada kididdiga da bayani game da masu laifin satar mutane da rundunar ta yi a shekarar 2021 da ta shude.

Kara karanta wannan

Katsina: Za mu dage dokar dakile layikan sadarwa kafin watan Janairun, Masari

Mutane 362 da ake zargi da fashi da makami da garkuwa da mutane aka kama a Kano a 2021. Bayan haka an kama barayi, 'yan damfara da masu safarar kwayoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel