Da Dumi-Dumi: Tsohon gwamnan mulkin soja, Anthony Obi, ya riga mu gidan gaskiya

Da Dumi-Dumi: Tsohon gwamnan mulkin soja, Anthony Obi, ya riga mu gidan gaskiya

  • Allah ya yi wa Kwanel Kwanel Anthony Uzoma Obi, tsohon gwamnan mulkin soja na jihohin Osun da Abia rasuwa
  • Marigayin ya rasu ne a ranar Asabar 1 ga watan Janairun 2022 misalin karfe 6.03 na yamma kamar yadda iyalansa suka sanar
  • Gboyega Oyetola, gwamnan jihar Osun mai ci a yanzu ya mika sakon ta'aziyya ga iyalen mamacin tare da fatan Allah ya yi masa rahama

Jihar Osun - Tsohon gwamnan zamanin mulkin soja na jihar Osun, Kwanel Anthony Uzoma Obi (mai ritaya) ya rasu, Vanguard ta ruwaito.

Iyalansa ne suka fitar da sanarwar rasuwarsa kamar yadda sake zuwa a ruwayar NewsWireNGR.

Da Dumi-Dumi: Tsohon gwamnan mulkin soja, Anthony Obi, ya riga mu gidan gaskiya
Allah ya yi wa tsohon gwamnan mulkin soja, Anthony Obi, rasuwa. Hoto: Vanguard
Asali: Facebook

Wani sashi na sanarwar ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Daga karshe: Shehu Sani ya bayyana aniyar tsayawa takarar gwamna, ya fadi manufarsa

"Mu iyalan mai girma, Kwanel Anthony Uzoma Obi (mai ritaya) muna sanar da rasuwar shugaban iyalinmu a ranar Asabar 1 ga watan Janairun 2022 misalin karfe 6.03 na yamma.
"Mahaifin mu jarumi ne, gwarzon soja wanda ya yi wa kasarsa hidima a matsayin gwamna na mulkin soja a jihohin Osun da Abia a Najeriya.
"Muna rokon addu'a da sakon jajentawa a wannan lokaci mai wahala da iyalan mu ke ciki.
"Muna bankwana da Kwanel A.U. Obi, iyalanka ba za su taba mantawa da kai ba da izinin Allah."

Gwamnan Osun Gboyega Oyetola ya mika mika sakon ta'aziyya ga iyalan Obi

A sakonsa na ta'aziyya ga iyalan mamacin, Oyetola ya yi alhinin rasuwar tsohon gwamnan mulkin sojan.

Oyetola ya jajantawa iyalan Obi sannan ya yaba wa gudunmawa da ya bada wurin gina jihar Osun.

Ya ce Obi na daya daga cikin wadanda suka kafa turbar gina jihar.

Ya yi addu'ar Allah ya jikan mamacin ya sa ya huta sannan ya bawa iyalansa hakurin jure wannan babban rashin.

Kara karanta wannan

Kwankwaso: Babu shakka an yi wa Ganduje warwas a zaben 2019, masu iko suka makala wa Kano

Idan ba a manta ba Obi ya yi aiki a matsayin gwamnan mulkin soja a jihar Osun daga Augustan 1996 zuwa Augustan 1998.

Bashir Tofa, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Zaɓen 1993, Ya Rasu

A wani labarin mai kama da wannan, Alhaji Bashir Tofa, ɗaya daga cikin ƴan takarar shugaban kasa a zaben 1993, wanda ake yi wa kallon zabe mafi adalci a Najeriya, ya rasu kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

A cewar majiyoyi daga yan uwansa, Tofa ya rasu ne a asibitin koyarwa ta Aminu Kano, AKTH, a safiyar ranar Litinin bayan gajeruwar lafiya, The Cable ta ruwaito.

Da ya ke tabbatar da rasuwarsa, dan uwan marigayin ya ce, "Alhaji Bashir Tofa ya rasu bayan gajeruwar rashin lafiya."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel